Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ɗaukacin ‘yan Nijeriya da ke zaune a ƙasar Iran da sauran ƙasashen yankin tekun fasha (Gulf) da su kasance cikin...
A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar a ranar Asabar, 28 ga Fabrairu, 2026, wacce Kakakin ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, gwamnatin ta bayyana cewa tana sanya idanu sosai kan yadda al’amura ke sauyawa bayan hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai kan wasu wurare a Iran, da kuma martanin da ita ma Iran ɗin ta mayar.
Don tabbatar da tsira da lafiyar ‘yan ƙasa, ma’aikatar ta fitar da wasu shawarwari guda biyar (5) kamar haka:
* Gwamnati ta shawarci ‘yan Nijeriya da su guji zirga-zirga a kusa da sansanonin soji, gine-ginen gwamnati, ko wuraren da ake ganin za su iya zama matattarar rikici.
* An buƙaci mutane da su zauna a gida muddin ba wata muhimmiyar buƙata ce ta fitar da su ba, sannan su guji shiga taron jama’a ko zanga-zanga.
* An buƙaci ‘yan ƙasa da su kiyaye dukkan dokoki da matakan tsaro da hukumomin ƙasashen da suke ciki suka gindaya.
* Ma’aikatar ta buƙaci mutane da su rinƙa sauraron kafafen yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa masu gaskiya, sannan su kiyayi yaɗa labaran bogi (fake news).
* Sanarwar ta tabbatar da cewa ofisoshin jakadancin Nijeriya da ke Tehran (Iran), Qatar, Bahrain, Kuwait, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), da Saudi Arabiya suna cikin shirin ko-ta-kwana don tallafa wa duk wani ɗan Nijeriya da ya shiga cikin matsala.
A ƙarshe, Gwamnatin Nijeriya ta yi kira ga ɗaukacin bangarorin da rikicin ya shafa da su kwantar da hankalin su, su ajiye makamai su koma kan teburin tattaunawa domin samar da zaman lafiya a duniya.
Ta kuma sake jaddada cewa kare rayukan ‘yan Nijeriya a duk inda suke a faɗin duniya shi ne babban burin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

No comments