Taron Fabrairu na Kwamitin Manufofin Kuɗi (MPC) na Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya nuna muhimmin sauyi a tsarin manufofin kuɗin Nijeriya. Du...
1. Tsauraran Manufofin Kuɗi Sun Fara Nuna Tasiri
Rage kuɗin ruwa na nuna cewa CBN na ganin tsauraran matakan da aka ɗauka a baya sun fara bada sakamako. Bayan watanni na ƙarin kuɗin ruwa domin daƙile hauhawar farashi, yanzu ana ganin alamu na sauƙi a matsin farashi.
Kwamitin ya jaddada cewa wannan sauƙin ya samo asali ne daga jinkirin tasirin manufofin da aka aiwatar a baya.
Manufofin kuɗi kan ɗauki lokaci kafin su bayyana a tattalin arziƙi, kuma sabbin bayanan farashi sun ba masu tsara manufofi ƙwarin gwiwar sassauta kaɗan ba tare da samun cika a taka-tsantsan da CBN ake yi ba.
2. Daidaiton Canjin Kuɗi Ya Ba da Damar Sassauta Kuɗin Ruwa
Daidaiton darajar naira ya taka muhimmiyar rawa a wannan shawara. Ingantacciyar wadatar kuɗaɗen waje, ƙarin shigowar jarin waje, da daidaitattun kuɗaɗen da ‘yan Nijeriya ke turowa daga ƙasashen waje sun taimaka wajen ƙarfafa naira da ajiyar kuɗaɗen waje.
CBN ya bayyana cewa asusun ajiyar kuɗin ƙasar ke rage haɗarin girgizar tattalin arziƙin waje. Wannan kariya ce da ta rage yiwuwar matsin lamba ga kuɗi bayan rage kuɗin ruwa.
3. Wadatar Abinci Na Taimaka Wa Rage Hauhawar Farashi
Tunda abinci na da babban kaso a ma’aunin farashin kaya, sauye-sauyen ɓangaren noma na da tasiri kai tsaye ga hauhawar farashi. CBN ya lura da cewa ƙarin wadatar hatsi kamar shinkafa, masara, gero, da waken soya, tare da daidaiton farashin mai, sun taimaka wajen rage hauhawar farashin abinci.
Wannan na nuna cewa kuɗin ruwa kaɗai ba zai iya magance hauhawar farashi ba a tattalin arziƙin da abinci ke da tasiri mai yawa. Samar da abinci, sufuri, ajiya, da farashin makamashi duk suna taka rawa.
4. Ƙarfafa Jarin Bankuna Na Da Muhimmanci ga Ci Gaban Tattalin Arziƙi
Kwamitin ya kuma duba shirin ƙara jarin bankuna. A cewar sanarwar, bankuna 33 sun samu ƙarin jari, yayin da 20 suka cika sabbin ƙa’idojin mafi ƙarancin jari.
Daga cikin bankunan da suka cika sharuddan akwai Zenith Bank, United Bank for Africa, First Bank of Nigeria, Fidelity Bank, da Guaranty Trust Bank.
CBN ya bayyana cewa ƙarfafa jarin bankuna zai inganta ikon su wajen bayar da rance da tallafawa faɗaɗar tattalin arziƙin, musamman yayin da gwamnati ke burin bunƙasa tattalin arziƙi zuwa dala tiriliyan ɗaya daga nan zuwa shekarar 2030.
5. Buƙatar Yin Taka-Tsantsan Duk da Sassautawa
Duk da rage kuɗin ruwa, MPC ya nuna taka-tsantsan. Ya yi gargaɗi kan yiwuwar sake tashin farashi sakamakon ƙarin kashe kuɗin gwamnati da rashin tabbas a tattalin arziƙin duniya.
Rage kuɗin ruwa da daga kaso 27% zuwa 26.50 ya nuna cewa matakin sassautawa suna da iyaka. Kwamitin ya jaddada cewa manufofin za su ci gaba da kasancewa bisa bayanai, tare da sa-ido kan sabbin sauye-sauye.
Hasashen Nan Gaba
CBN na hasashen matsakaicin hauhawar farashi na 2026 zai kai 12.94%, wanda ake sa ran zai samu tallafi daga raguwar farashin abinci da yiwuwar sauƙin farashin man fetur.
Sai dai kuma, ƙarin kashe kuɗin gwamnati na iya zama barazana ga wannan hasashe. Saboda haka, taron Fabrairu ya fi nuna gyara cikin taka-tsantsan maimakon sauyi gaba ɗaya.
Masu karɓar rance daga bankunan kasuwanci na iya samun ɗan sauƙi. Cimma farashi mai kwanciyar hankali zai buƙaci daidaito tsakanin manufofin kuɗi da na kasafin kuɗi. Wannan kuwa duk irin ƙoƙarin da CBN ke yi ne domin ci gaba da ɗora tattalin arziƙin Nijeriya bisa miƙaƙar hanya.

No comments