Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada ƙudirin Nijeriya na ƙarfafa dangantakar ta da Masarautar Saudi...
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Jakaden Saudiyya a Nijeriya, Yosef Bin Mohammed Al Balawi, tare da tawagar sa a hedikwatar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya da ke Abuja a ranar Laraba.
Yayin da yake maraba da Jakaden, Ministan ya bayyana ziyarar a matsayin wani muhimmin mataki na zurfafa haɗin gwiwar hukumomi tsakanin ƙasashen biyu.
Ya jaddada cewa Nijeriya na daraja dangantakar ta mai ɗorewa da Saudiyya, kuma ta himmatu wajen faɗaɗa haɗin kai a muhimman fannoni.
Ya ce: “Nijeriya tana darajta dangantakar ta mai daɗaɗɗen tarihi da Masarautar Saudiyya, kuma mun ƙudiri aniyar mayar da tarihin haɗin kan mu zuwa ƙarfafa hulɗodin hukumomi, musamman a fannonin haɗin gwiwar kafofin yaɗa labarai, tattalin arziki da harkokin tsaro domin amfanin al’ummomin mu."
Ministan ya bayyana cewa Nijeriya ta amince da manyan Takardun Yarjejeniyar Fahimtar Juna guda uku (MOUs) da hukumomin Saudiyya suka gabatar domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin yaɗa labarai da sadarwa.
Waɗannan sun haɗa da musayar labarai tsakanin Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) da Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya, haɗin gwiwa wajen watsa shirye-shiryen rediyo da talbijin tsakanin Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA) da Hukumar Watsa Labarai ta Saudiyya, da kuma haɗin gwiwa a fannin kafafen yaɗa labarai na sauti da gani tsakanin Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Nijeriya (NBC) da hukumomin da suka dace a Masarautar.
A cewar sa, waɗannan yarjejeniyoyi za su ƙarfafa musayar ƙwarewa, inganta daidaitaccen yaɗa bayanai, da kuma bunƙasa diflomasiyyar kafofin yaɗa labarai tsakanin ƙasashen biyu.
Ya ce: “Takardun Yarjejeniyar Fahimtar Juna tsakanin cibiyoyin mu na yaɗa labarai ba takardu ba ne kawai; suna wakiltar wani muhimmin mataki na ƙarfafa diflomasiyyar kafofin yaɗa labarai, inganta musayar sahihan bayanai, da zurfafa dangantakar ƙasashen mu.”
Ministan ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwa a dandamalin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa irin su Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi (OIC) da UNESCO, inda ƙasashen biyu suke da muradu iri ɗaya.
Ya ce Nijeriya tana da niyyar yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Saudiyya wajen inganta zaman lafiya a duniya, tattaunawar al’adu, da cigaba mai ɗorewa.
Yayin da ya amince da ƙaƙƙarfar alaƙar addini da al’adu tsakanin ƙasashen biyu, Ministan ya yi godiya ga Saudiyya bisa ci gaba da tallafa wa harkokin aikin Hajji da Umrah ga maniyyata ‘yan Nijeriya.
Ya kuma yi maraba da tattaunawar da ake yi kan yiwuwar dawo da jiragen sama kai-tsaye tsakanin Jiddah da Abuja, yana mai cewa hakan zai ƙara ƙarfafa hulɗar jama’a da jama’a, yawon buɗe ido da musayar tattalin arziki.
A nasa jawabin tun da farko, Jakada Yosef bin Mohammed Al Balawi ya nuna godiya bisa kyakkyawar tarbar da aka yi masa, tare da isar da muradin ƙasar sa na ƙarfafa haɗin gwiwa da Nijeriya a muhimman fannoni da suka haɗa da tattalin arziki, tsaro, yaɗa labarai da dangantakar siyasa.
“Saudiyya tana ɗokin yin aiki tare da Nijeriya domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannonin yaɗa labarai, tattalin arziki, tsaro da harkokin addini, tare da tabbatar da cewa ana yaɗa sahihan bayanai masu ma’ana game da ƙasar mu ta hanyar ƙarfafa hulɗodin hukumomi,” inji Jakaden.
Jakaden ya kuma sake jaddada aniyar Saudiyya na ci gaba da hidimta wa maniyyatan Nijeriya, tare da bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin inganta haɗin kai da sauƙaƙa zirga-zirga domin amfanin al’ummomin ƙasashen biyu.
Waɗanda suka halarci zaman ziyarar sun haɗa da Babban Sakataren Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Ogbodo Chinasa Nnam; Daraktan Sadarwar Jama’a, Henshaw Ogubike; Daraktan Hulɗa da Jama’a da Tsare-tsare, Dakta Suleiman Haruna; Daraktar Cibiyar Adana Takardun Ƙasa, Dakta Evelyn Odigboh, da sauran su.

No comments