Shugaban Amurka Donald Trump ya sake tsallake rijiya da baya bayan da wani mutum ɗauke da makami ya kutsa cikin jami'an tsaro na gidansa...
Shugaban Amurka Donald Trump ya sake tsallake rijiya da baya bayan da wani mutum ɗauke da makami ya kutsa cikin jami'an tsaro na gidansa da ke Mar-a-Lago a jihar Florida, inda jami’an tsaro suka harbe shi har lahira.
A cewar jami'an tsaron shugaban ƙasa na United States Secret Service, mutumin – wanda aka bayyana a matsayin farar fata – na ɗauke da bindiga cike da alburusai da kuma galan man fetur lokacin da aka hango shi kusa da ƙofar arewa ta harabar gidan. Rahotanni sun ce Trump bai kasance a Florida a lokacin da lamarin ya faru ba.
Har yanzu ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa mutumin ya kutsa cikin tsaron ba, amma wannan ba shi ne karon farko da jami’an tsaro ke tinkarar barazana yayin da suke kare Trump ba.
A watan Satumban 2024, wani jami’in tsaro ya hango bindiga a cikin bishiyoyi a filin wasan golf na Trump International da ke West Palm Beach. Mutumin, wanda daga baya aka gano sunansa Ryan Routh, ya yi kokarin tserewa amma aka kama shi. A watan Fabrairun 2026, kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai bisa yunkurin kashe shugaban.
Haka kuma, a watan Yulin 2024, wani matashi mai shekaru 20 mai suna Thomas Matthew Crooks ya bude wuta yayin wani gangamin yakin neman zabe a Butler, Pennsylvania. An kashe shi a wurin, yayin da mutum daya ya rasa ransa, wasu biyu suka jikkata, kuma Trump ya samu rauni a kunne.
Gidan Mar-a-Lago, wanda aka fi sani da “Fadar Fari ta Hunturu,” shi ne mazaunin Trump a Florida. Ya sayi katafaren gidan mai salon gine-ginen Sifaniyanci a shekarar 1985 kan dala miliyan 10, inda daga bisani ya mayar da shi wurin hutu na iyalinsa a lokacin sanyi. Tun daga lokacin da ya hau mulki, Trump ya rika amfani da wurin wajen karbar bakuncin shugabannin duniya, fitattun mutane da manyan ‘yan kasuwa.
An gina Mar-a-Lago tun a shekarar 1927, kuma baya ga zama gidan shugaban, har ila yau cibiyar kulob ce ta masu zaman kansu, inda mambobi ke da damar shiga sassan harabar, ban da bangaren da iyalan Trump ke zama.
Lamarin na baya-bayan nan ya sake jaddada kalubalen tsaro da ke tattare da kare manyan shugabanni, musamman a lokacin da yanayin siyasa ke da zafi a Amurka.

No comments