Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga gwamnonin jihohi da shugabannin addinin Musulunci da Kiristanci da su ƙara karkata manufofinsu wajen...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga gwamnonin jihohi da shugabannin addinin Musulunci da Kiristanci da su ƙara karkata manufofinsu wajen tallafa wa talakawa da marasa galihu, domin a cewarsa ci gaba ba zai yi ma’ana ba idan bai sauka har matakin ƙasa ba.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, yayin da ya karɓi baƙuncin gwamnonin jihohi domin buda-baki na haɗin gwiwar addinai. Ya ce haɗuwar azumin Ramadan da na Kiristoci (Lent) a lokaci guda alama ce ta ɗan’adamtaka ɗaya, wadda ke buƙatar juriya, sadaukarwa da kaunar juna.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa watan Ramadan da lokacin Lent dama ce ga shugabanni su sake duba halin da jama’a ke ciki, musamman matasa da marasa galihu, tare da ƙirƙiro shirye-shiryen da za su shafi rayuwarsu kai tsaye. Ya jaddada cewa duk da nasarorin da aka samu, akwai sauran aiki mai yawa a fannin rage talauci da ƙarfafawa matasa.
A jawabinsa, shugaban ya buƙaci gwamnonin su kasance masu haƙuri da juna, su gina tsari a wannan lokaci na bangaskiya da haɗin kai, tare da bai wa matasa damar numfasawa. Ya kuma yi maraba da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya yi masa maraba cikin raha.
Haka nan, Shugaba Tinubu ya yaba wa Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, bisa nuna karamci ga Musulmi da Kiristoci a lokacin azumi, musamman ta hanyar shirye-shiryen tallafin Ramadan da suka shafi kowa ba tare da la’akari da addini ba.
Shugaban ya sake nanata aniyarsa ta ƙarfafa tsaro a ƙasar nan, inda ya ce gwamnati ba za ta jinkirta cika alƙawarin kafa ‘yan sandan jihohi ba, domin a magance matsalar rashin tsaro. Ya ce tsaro shi ne ginshiƙin bunƙasar tattalin arziƙi, domin noma, kasuwanci da zaman lafiya su bunƙasa.
Da yake jawabi a madadin Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya yabawa Shugaba Tinubu bisa yadda yake ƙarfafa haɗin kan yan ƙasa duk da bambance-bambancen addini da ƙabila. Ya ce haɗuwar azumin Ramadan da Lent abu ne na musamman da Allah Ya tsara domin tunatar da Musulmi da Kiristoci muhimmancin haɗin kai da tausayi.
Uzodimma ya ƙara da cewa shugabancin Shugaba Tinubu ya kawo sauye-sauye masu muhimmanci a siyasar ƙasa, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi. Ya ce wannan lokaci na azumi lokaci ne na taimakon marasa galihu, kuma taron buda-baki na haɗin kan addinai alama ce ta wannan ruhi na haɗin kai.





No comments