Kwamitin Tsare-tsaren Kuɗi (MPC) na Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya rage Ƙayyadadden Adadin Kuɗin Ruwa (MPR) daga kashi 27% bisa 100% zuwa 2...
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ne ya sanar da rage kuɗin ruwan a wani taron manema labarai ranar Talata, yayin taron MPC na 304 da aka gudanar a Abuja.
Wannan ragi shi ne mafi ƙanƙanta tun bayan taron watan Mayu 2024, lokacin da kuɗin ruwan ya kasance 26.25%.
MPR shi ne babban ma’aunin geji da adadin kuɗin ruwa a tattalin arziki, domin yawancin sauran kuɗaɗen ruwa a ƙasa ana gina su ne a kan sa.
Dalilan Rage Kuɗin Ruwa
Matakin MPC ya biyo bayan saukar hauhawar farashin kayan masarufi da na amfanin yau da kullum a Nijeriya zuwa 15.1% a Fabrairu 2026.
Haka kuma, wannan na zuwa ne watanni shida bayan da aka rage kuɗin ruwan zuwa 27% a Satumba 2025.
A wajen taron manema labarai, Cardoso ya ce mambobin kwamitin sun amince baki ɗaya da rage kkuɗinruwan da maki 50 daga 27% zuwa 26.5%, yayin da aka bar sauran tsare-tsare gejin adadin manufofin kuɗaɗe ba tare da canji ba.
Sauran Muhimman Tsare-tsare
Gwamnan CBN ya bayyana cewa:
Adadin Tsabar Kuɗi da bankunan kasuwanci za su riƙa ajiyewa, ba tare da sun bayar da su lamuni ba wato 'Cash Reserve Ratio' (CRR) zai ci gaba da kasancewa:
45% bisa 100.
Su kuma bankunan 'marchant', na su adadin zai kasance kashi 16%.
Haka kuma a wurin taron an amince da kashi 75% matsayin adadin kuɗaɗen da ma'aikatun gwamnati, cibiyoyi da hukumomi za su riƙa ajiyewa a asusun ajiyar kuɗaɗen gwamnati da ba na bai-ɗaya ba, wato non-TSA.
An Amince Da Kashi 30% Matsayin Kuɗin Lukudin (Liquidity Ratio)
Dukkannin mambobin kwamitin a ta bakin Cardoso, sun bar wannnan geji wajejan +50/-450 na adadin ƙayyadadden kuɗin ruwa.
Kwamitin ya ce an yanke shawarar ne bayan cikakken nazari kan haɗurran tattalin arziki, wanda ke nuna cewa saukar hauhawar farashi na ci gaba.
Cardoso ya ƙara da cewa malejin ƙididdigar saukar farashi saukar a muzanin tsakanin wannan shekara da ta bayan ta, wato shekara-shekara a Janairu 2026, ya zama karo na 11 a jere kenan yana sauka tare da samun raguwa.
Hasashen Gaba
CBN ya bayyana cewa ana sa ran ƙarin saukar hauhawar farashi zai ci gaba, sakamakon wanzuwar darajar canjin kuɗi da kuma ingantuwar wadatar abinci.
Sai dai Cardoso ya yi gargaɗi cewa ƙarin kashe-kashen maƙudan kuɗaɗe musamman masu nasaba da zaɓe mai zuwa na 2027, na iya haifar da hauhawar farashi nan gaba.
Karuwar Ajiyar Kuɗaɗen Waje
CBN ya kuma bayyana cewa gejin adadin ajiyar kuɗaɗen waje ya kai dala biliyan 50.45 zuwa ranar 16 ga Fabrairu 2026. Wannan adadi kuwa shi ne mafi girma cikin shekaru 13.
Kwamitin ya danganta wannan da:
Ƙarin kuɗaɗen shiga daga fitar da kaya waje,
ƙarin kuɗaɗen turo kuɗi daga ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje, wato remittance
da kuma saitin da kasuwar canjin kuɗi ta ɗauka yanzu, inda Naira ke ci gaba da samun tagomashi.
Cardoso ya ce wannan ci gaban ya taimaka wajen daidaita tsammanin kasuwa da kuma rage hauhawar farashi.

No comments