Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

IPAC KADUNA: INEC Ta Jaddada Sahihancin Zaben Mikail Abubakar, Ta Yi Watsi Da Duk Wani Ba Shi Ba

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa ba ta da hannu a wani zabe da ake zargin an gudanar a matsayin zaben shugabanci...

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa ba ta da hannu a wani zabe da ake zargin an gudanar a matsayin zaben shugabancin Ƙungiyar Jam'iyyun Siyasa (IPAC), reshen jihar Kaduna, inda ta tabbatar da cewa zabe guda ɗaya kacal ta sanya ido a kansa, wanda kuma Mikail Abubakar ne ya zama shugaba.

A cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishinta, INEC ta ce zaben da ta amince da shi shi ne wanda Kwamitin Zabe na Ƙasa na IPAC ya gudanar a ɗakin taro na INEC da ke Kaduna, tare da sanya idon jami’an hukumar.

Hukumar ta jaddada cewa duk wani zabe da aka gudanar sabanin wannan, to ba ta da masaniya a kansa, kuma ba shi da inganci a idonta.

A ranar Alhamis da ta gabata ne INEC ta sanya ido kan zaben IPAC na jihar Kaduna, wanda ya haifar da zaben ɗan jam'iyyar YPP, Mikailu Abubakar, a matsayin shugaban IPAC na jihar.

Sai dai wasu mutane ƙalilan sun gudanar da wani zabe daban, ba tare da halartar jami’an INEC ba, inda suka bayyana Ahmed Tijjani Mustapha a matsayin shugaban IPAC na Kaduna. Wannan mataki ya janyo cece-kuce tsakanin bangarorin siyasa a jihar.

Da yake ƙarin haske, Shugaban Sashen Ayyukan Zabe na INEC, Mohammed Ismail, ya tabbatar da cewa zabe guda ɗaya ne kawai hukumar ta sanya ido a kansa.

“Zaben da muka sanya ido a kansa shi ne kaɗai muka sani,” in ji shi, yana mai jaddada cewa duk wani abu da ya sabawa haka bai shafi hukumar ba.

Tun da farko, bayan kammala zaben a hedikwatar INEC da ke Kaduna, Mohammed Ismail ya bayyana cewa tsarin da ya haifar da shugabancin Mikailu Abubakar da sauran ‘yan kwamitinsa ya kasance mai gaskiya da bin ƙa’ida, tare da nuna cewa an gudanar da shi cikin tsari da gaskiya.

Matakin INEC na fayyace matsayinta ya zo ne domin kauce wa ruɗani da tabbatar da cewa an kiyaye doka da oda a harkokin tafiyar da al’amuran jam’iyyun siyasa a jihar.






No comments