Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Babu Inda Gwamnatin Tarayya Ta Biya Kuɗin Fansa Don Sako Ɗaliban Neja -Minista

Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin cewa sai da ta biya kuɗin fansa tare da sakin kwamandojin ’yan ta’adda domin a saki ɗaliban makarantar k...


Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin cewa sai da ta biya kuɗin fansa tare da sakin kwamandojin ’yan ta’adda domin a saki ɗaliban makarantar kwana ta St. Mary’s da aka sace a Jihar Neja.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, yana mayar da martani ga wani rahoto da ke yawo a kafafen yaɗa labarai, wanda aka danganta da wasu kafafen yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa.

Rahoton ya yi zargin cewa Gwamnatin Nijeriya ta biya gagarumin kuɗin fansa domin a sako ɗaliban.

Sai dai Gwamnatin Tarayya ta bayyana zargin a matsayin “ƙarya ce tsagwaron ta kuma ba ta da tushe,” tana mai cewa hakan “na ɓata suna da ƙwarewar jami’an tsaron Nijeriya tare da raina sadaukarwar da suke yi a kullum.”

Gwamnatin ta ce duk da yake tana mutunta ’yancin ’yan jarida, “ta yi watsi da wannan labari, daga wasu majiyoyin da ba a bayyana sunayen su ba, waɗanda suke ƙoƙarin raunana amincin gwamnati mai cin gashin kan ta wadda ke aiki bisa dokokin ta.”

Ta ƙara da cewa, “Domin kawar da duk wani shakku, ba a biya ko sisin kwabo na kuɗin fansa ba, kuma ba a saki wani kwamandan ’yan ta’adda ba.”

Ministan ya ce zarge-zargen sun dogara gaba ɗaya ne kan wasu majiyoyin bayanan leƙen asiri da ba a bayyana sunayen su ba da kuma wasu da aka bayyana a matsayin “masu masaniya kan tattaunawar,” abin da ke saɓani da musantawar da hukumomin da suka dace suka yi a fili.

Ya ce Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA), da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), da shugabannin Majalisar Dokoki duk sun fito fili sun musanta batun biyan kuɗin fansa.

Gwamnatin ta kuma ce rahoton ya ƙunshi saɓani a bayanan da ya gabatar dangane da zargin kuɗin fansa, lamarin da ya nuna zato kuma ya raunana sahihancin sa.

Game da wani zargi na musamman, ministan ya ce iƙirarin cewa an kai kuɗin fansa ta jirgi mai saukar ungulu ga ’yan tada ƙayar baya, tare da tabbatar da karɓar sa ta ƙetaren iyaka ƙarya ce.

Ya ƙara da cewa DSS ta yi watsi da wannan zargi a matsayin “ƙarya ce kuma abin dariya.”

Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa Nijeriya tana fuskantar wata tsararrar harkar laifi mai neman riba, tana mai cewa nasarar ceto ɗaliban ba tare da rasa rai ba ta samo asali ne daga ƙwarewar tattara bayanan sirri da kuma ingantaccen aikin rundunonin tsaro.

Ta kuma sake tabbatar da ƙudirin ta na ci gaba da tabbatar da tsaro a ƙasa, tare da kira ga kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafa rahotannin zato da ka iya ƙarfafa wa masu aikata laifi gwiwa ko raunana ƙwarin gwiwar jami’an tsaro.
 

No comments