Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Taya APC Murnar Nasara a Zaɓukan Birnin Tarayya, Jihar Kano Da Ribas

  Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya waɗanda suka yi nasara a zaɓukan da aka gudanar ranar Asabar a Babban Birnin Tarayya (FCT) da ji...


 
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya waɗanda suka yi nasara a zaɓukan da aka gudanar ranar Asabar a Babban Birnin Tarayya (FCT) da jihohin Kano da Ribas murna.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, Independent National Electoral Commission (INEC), ce ta gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomi shida na FCT, tare da zaɓen cike gurbi a mazabun Ahoada East II da Khana II na Jihar Ribas, da kuma mazabun Kano Municipal da Ungogo a Jihar Kano.

Shugaba Tinubu ya buƙaci waɗanda suka lashe zaɓen da su yi aiki da kyautatawa, kishin ƙasa da kuma sadaukar da kai, yana mai jaddada cewa amanar da al’umma suka ba su wata amana ce mai tsarki da ya wajaba su kiyaye.

Haka kuma, ya yabawa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bisa irin nasarorin da ya samu a yankin, wanda ya ce sun taimaka wajen samar wa jam’iyyar APC gagarumar nasara a zaɓen.

Shugaban ya kuma taya shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa, da na jihohin Kano da Ribas, tare da dukkan mambobin jam’iyyar, murnar nasarorin da aka samu a zaɓen.

Ya yabawa INEC, jami’an tsaro da masu kaɗa ƙuri’a bisa gudanar da zaɓen cikin lumana da nasara, tare da yaba wa dukkan ‘yan takarar da suka nuna jajircewa da bin doka yayin fafatawar zaɓen.

A cewarsa, nasarar gudanar da zaɓukan cikin nasara na ƙara ƙarfafa dimokuraɗiyya a ƙasar, yana mai kira ga INEC da ta ci gaba da inganta ayyukanta domin samar da sahihin tsarin zaɓe a nan gaba.

No comments