Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

RAMADAN: Shugaba Tinubu Ya Yi Kira Ga Musulmi Da Kirista Su Ƙarfafa Haɗin Kai Da Zaman Lafiya

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da Kirista a Najeriya da su yi amfani da watan Ramadan mai alfarma wajen ƙa...



Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da Kirista a Najeriya da su yi amfani da watan Ramadan mai alfarma wajen ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da fahimtar juna domin ci gaban ƙasa.

A cikin saƙon da ya fitar a ranar Laraba daga Birnin Tarayya Abuja, Shugaban Ƙasar ya bayyana cewa fara azumin Ramadan da na Lent a rana ɗaya a bana wata dama ce ta musamman ga ‘yan Najeriya su ƙara dankon zumunci da haɗin kai duk da bambancin addini.

Ya ce watan Ramadan lokaci ne na ibada, sadaukarwa da kyautatawa juna, wanda ya kamata a yi amfani da shi wajen gina zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

Shugaba Tinubu ya kuma jaddada muhimmancin kyautata hulɗa tsakanin mabambantan addinai, taimaka wa marasa galihu, gujewa duk wani abu da zai haddasa rarrabuwar kawuna da yin addu’o’i domin tsaro da ci gaban ƙasa

Ya buƙaci ‘yan ƙasa da su yi rayuwa bisa kyawawan koyarwar addinansu tare da nuna tausayi da haƙuri ga juna, yana mai cewa zaman lafiya da haɗin kai su ne ginshiƙan ci gaban kowace al’umma.

Shugaban ya kuma yi addu’ar cewa albarkar watan Ramadan za a kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaba a Najeriya.

No comments