Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shafe kwana uku a tsare a hannun Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Tu'ann...
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shafe kwana uku a tsare a hannun Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Tu'annati (EFCC) bisa zargin almundahana da karkatar da sama da Naira biliyan 433 a tsawon mulkinsa daga 2015 zuwa 2023.
Rahotanni sun nuna cewa EFCC ta amince da bayar da beli na wucin gadi, inda ta sharɗanta cewa sai Babban Sakataren Ma’aikata, wato Permanent Secretary da wani Darakta a ma’aikatar tarayya sun tsaya masa a matsayin masu tabbatarwa. Sai dai lamarin ya sauya alƙibla bayan da aka ce Babban Sakataren ya isa ofishin hukumar domin kammala sharuɗɗan belin, amma daga bisani aka dakatar da tsarin.
Majiyoyi sun bayyana cewa daga baya Babban Sakataren ya janye daga tsayawa belin ne bayan ya samu barazana, lamarin da ya haifar da zarge-zargen tsoratarwa da yiwuwar katsalandan a cikin shari’ar. Har zuwa yanzu, EFCC ba ta fitar da cikakken bayani a hukumance kan janyewar ba.
A gefe guda kuma, an shirya El-Rufai ya gurfana a gaban hukumar ICPC domin amsa tambayoyi kan wasu zarge-zargen da dama. Sai dai ba a tabbatar ko zai samu damar halartar gayyatar ba, ganin cewa har yanzu yana tsare a hannun EFCC. Lauyoyinsa sun rubuta wa ICPC wasiƙa suna sanar da halin da ake ciki.
Haka kuma, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta shigar da ƙara a babbar kotun tarayya da ke Abuja, tana zargin El-Rufai da kutse cikin wayar tarho ta Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu. A cikin takardun ƙarar, ana zargin cewa tsohon gwamnan ya amsa a wata hira da ya yi a gidan talabijin na Arise TV cewa ya sani kuma ya yi hulɗa da mutanen da suka yi kutsen, tare da gazawa wajen kai rahoto ga hukumomin tsaro.
Takardar ƙarar mai lamba FHC/CR/99/2026 ta ƙunshi tuhume-tuhume uku da suka shafi karya dokar yaƙi da laifukan yanar gizo ta 2024 da kuma dokar sadarwa ta 2003. Idan aka same shi da laifi, dokokin sun tanadi hukunci mai tsauri da ya haɗa da ɗaurin shekaru a gidan yari.
Batun janyewar Babban Sakataren daga tsayawa belin ya ƙara janyo cece-kuce a fagen siyasa da shari’a, inda wasu ke ganin barazanar da aka ambata ce ta tilasta masa ficewa, yayin da wasu ke kira da a gudanar da bincike cikin gaskiya ba tare da tsoma bakin siyasa ba.
Yanzu haka al’umma na zura ido domin ganin matakin da hukumomi za su ɗauka, yayin da shari’ar ke kara ɗaukar sabon salo a fagen siyasar ƙasa.

No comments