Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Tabbatar Da Cikakken Goyon Baya Ga Mukaddashin IGP Disu A Fannin Tsaro

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da cikakken goyon bayansa ga sabon mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Disu, domi...




Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da cikakken goyon bayansa ga sabon mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Disu, domin ƙarfafa tsaro da maido da zaman lafiya a faɗin ƙasar nan. 

Shugaban Ƙasar ya bayyana haka ne a yayin naɗa Disu a Fadar Shugaban Ƙasa, yana mai jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne babban abin fifikon gwamnatinsa.

Tinubu ya buƙaci Disu da ya jagoranci rundunar ’yan sanda cikin adalci da ƙwarewa, tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro domin shawo kan matsalolin ’yan bindiga, ta’addanci da sauran laifuka. 

Ya ce gwamnatinsa za ta ba da cikakken tallafi da haɗin kai don tabbatar da nasarar sabon mukaddashin IGP a wannan muhimmin aiki.

No comments