Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Kasuwar Singa Sun Gode Wa Gwamnatin Tarayya Bisa Tallafin Da Ta Bayar Bayan Gobarar Kasuwar

* Gwamnatin Tarayya Ta Basu Tabbacin Hana Sake Afkuwar Gobara Irin Wannan A Kasuwar ’Yan kasuwar Singa da ke Kano sun bayyana godiyarsu ga G...

* Gwamnatin Tarayya Ta Basu Tabbacin Hana Sake Afkuwar Gobara Irin Wannan A Kasuwar

’Yan kasuwar Singa da ke Kano sun bayyana godiyarsu ga Gwamnatin Tarayya bisa tallafin da ta bayar bayan gobarar da ta lalata sassan kasuwar, tare da jin daɗin tabbacin da gwamnati ta ba su na ɗaukar matakan hana sake afkuwar irin wannan ibtila’i. 

Godiyar ta fito ne yayin ziyarar tawagar Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Kano zuwa ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa a Abuja.

Da yake karɓar tawagar, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya tabbatar wa ’yan kasuwar cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya riga ya amince da tallafin Naira biliyan 5 domin rage radadin asarar da gobarar ta haifar a Kano Singer Market.

Ya ce an kammala dukkan takardun da suka wajaba domin fitar da kuɗin ta hannun Ma’aikatar Jin-ƙai, tare da umarnin a rarraba su cikin gaskiya da adalci.

Shettima ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya, tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Kano da hukumomin da abin ya shafa, za ta ɗauki matakan kariya na kashe gobara domin hana sake afkuwar irin wannan lamarin.

A cewar sa, gwamnati za ta yi aiki da ƙungiyar ’yan kasuwar wajen inganta hanyoyin tsaro da tanadin kayan kashe gobara don kare rayuka da dukiyoyi.

A nasu ɓangaren, ’yan kasuwar sun jinjina wa gwamnatin Tarayya kan gaggawar tallafi da nuna tausayi, inda suka ce hakan ya farfaɗo da fata da kwarin gwiwa a zukatansu.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Sabiu Bako, ya roƙi a ƙara tallafi ta hanyar rancen kuɗi mara ruwa da kuma gyaran muhimman ababen more rayuwa a kasuwar, yana mai cewa Singa za ta tashi tsaye nan ba da jimawa ba, ta zama mafi aminci kuma mafi ƙarfi fiye da da.





 

No comments