Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya ce sauye-sauyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar sun ceci aƙa...
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya ce sauye-sauyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar sun ceci aƙalla jihohi 27 a Najeriya daga faɗawa cikin mummunan durƙushewar tattalin arziƙi.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake gabatar da lacca a bikin yaye ɗalibai karo na 34 da kuma cikar Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Minna shekaru 43 da kafuwa.
A cewar ministan, kafin hawan Shugaba Tinubu kan mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, kusan jihohi 27 ba sa iya biyan albashin ma’aikatansu. Ya ce Tinubu ya yi yawon neman zaɓe a faɗin ƙasar nan tare da tsare-tsaren farfaɗo da Najeriya, kuma bayan ya karɓi mulki ya ƙaddamar da muhimman gyare-gyare da suka ceci waɗannan jihohi daga rugujewa.
“Yanzu jihohi na samun ninki uku na abin da suke samu a da. Hakan ya ba su damar biyan albashi, aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa da kuma kai romon dimokiraɗiyya ga al’ummarsu,” in ji Mohammed Idris.
Ministan ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya fahimci cewa babu yadda za a gina ƙasa sai da ci gaba da yin sauye-sauye domin gyara kura-kuran baya da kuma ciyar da tsarin gina ƙasa gaba. Ya jaddada cewa rashin yin wannan sauyin na iya jefa ƙasa cikin wani mummunan hali, amma aiwatar da su a yanzu sun taimaka wajen kare Najeriya daga faɗawa tarkon durƙushewar tattalin arziƙi.

No comments