Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Babban Limamin Cocin Canterbury Ya Yaba da Dawowar Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Kaduna

Babban Limamin Cocin Canterbury,  Archbishop Justin Portal Welby, ya yaba wa Jihar Kaduna bisa gagarumin ci gaban da ta samu wajen dawo da z...



Babban Limamin Cocin Canterbury,  Archbishop Justin Portal Welby, ya yaba wa Jihar Kaduna bisa gagarumin ci gaban da ta samu wajen dawo da zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali karkashin jagorancin gwamna Uba Sani.

 Malamin yace jihar  Kaduna ta yi nesa da rikice-rikicen addini da ƙabilanci da suka taɓa shahara a kanta a baya inda yace hakan abin a yaba ne.

Archbishop Welby ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara ta girmamawa da ya kai Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna  jim kadan bayan kammala shirin da ya halarta a matsayin Babban Baƙon Jawabi a Laccar Taron Yaye Dalibai na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

Malamin addnin kirista. Yayi waiwaye kan ziyararsa ta farko zuwa Kaduna a shekarar 2002, Archbishop Welby ya tuna wani lokaci da jihar ke fama da rarrabuwar kawuna da rikice-rikice masu maimaituwa. 

Ya ce bambancin da ke tsakanin wancan lokaci da halin da ake ciki a yanzu na nutsuwa da zaman tare ne ya sa ya yanke shawarar kai ziyara Gidan Gwamnati, inda ya bayyana yanayin da ake ciki a yau a matsayin sakamakon ƙoƙari na sulhu da shugabanci mai haɗa kai.

A cewarsa, ci gaban da aka samu a Kaduna a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani ya zama abin ƙarfafawa ga shugabanni da al’ummomi da su ci gaba da jajircewa wajen gina zaman lafiya, tattaunawa da fahimtar juna, musamman a al’ummomin da ke da bambancin addini da ƙabila.

Da yake nasa jawabin, Gwamna Uba Sani ya nuna godiyarsa bisa ziyarar da kalaman yabo da Archbishop Welby ya yi, yana mai cewa hakan babbar karramawa ce kuma tabbaci ne ga ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen samar da zaman lafiya.

Gwamnan ya bayyana Tsarin Zaman Lafiya na Kaduna mai yake  (Kaduna Peace Model), wanda ya ce ya ta’allaka ne kan tattaunawa, haɗa kowa da kowa, adalci da daidaito, kuma shi ne ginshikin tafiyar gwamnatinsa cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata.

Ya jaddada cewa rashin samun rikice-rikicen addini da ƙabilanci a wannan lokaci a jihar da a da aka san ta da irin waɗannan matsaloli, ya samo asali ne daga manufofi na gangan da kuma tsayuwar daka wajen mulki mai haɗa kai wanda ke ƙin rarrabuwar kawuna ta fuskar asali ko addini.

Gwamna Uba Sani ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta fifita tattaunawa a kan rikici, shigar kowa cikin al’amura a kan warewa, da kuma ci gaban da ya shafi dukkan al’ummomi, da nufin mayar da tsoro ya zama amincewa da kuma gina manufar bai ɗaya a tsakanin jama’a.

Gwamnan  ya tabbatar da cewa Jihar Kaduna za ta ci gaba da ƙarfafa nasarorin zaman lafiya, inganta haɗin kai duk da bambance-bambance, tare da gina makoma da ta ta’allaka kan ci gaba na bai ɗaya, zaman tare da ci gaba mai direwa.

No comments