Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rahoton Kwamitocin Majalisar Wakilai Na Amurka Wata Dama Ce Ta Ƙarfafa Haɗin Gwiwa – Idris

  Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana rahoton da Kwamitocin Majalisar Wakilai biyu na Amurka suka fitar...

 


Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana rahoton da Kwamitocin Majalisar Wakilai biyu na Amurka suka fitar kan tsangwamar Kiristoci a Nijeriya a matsayin wata dama ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

Idris ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, bayan tattaunawa da aka yi a Majalisar Dokoki ta Amurka.

Rahoton, wanda Kwamitin Harkokin Waje da Kwamitin Kasafin Kudi suka miƙa wa Fadar White House a ranar Litinin, ya taɓo al’amuran tsaro a Nijeriya.

Ministan ya ce, “Gwamnatin Tarayya na sane da cewa wasu yankuna na ƙasa suna fuskantar manyan ƙalubalen tsaro, ciki har da ta’addanci, fashi da makami, da rikice-rikicen ƙabilanci waɗanda suka shafi al’ummomi da dama.”

Ya kuma jaddada damuwar Gwamnatin Tarayya kan asarar rayuka da lalacewar dukiya da waɗannan laifuka suka haifar, tare da jaje ga duk wanda abin ya shafa da iyalansa, ba tare da la’akari da addini, ƙabila ko yanki ba.

“Yana da muhimmanci a fayyace cewa Nijeriya ba ta da, kuma ba ta taɓa samun, manufofin gwamnati na tsangwamar addini ba,” inji Idris.

Ministan ya ƙara da cewa, “Ta’addancin da hukumomin tsaronmu ke yaƙa ba ya samo asali ne daga daga manufofin gwamnati ko son kai na addini ba, sai dai daga barazanar tsaro, ciki har da ta’addanci, laifukan da aka tsara, da rikice-rikicen ƙabilanci da suka daɗe.”

Ya kuma jaddada cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya yana tabbatar da ‘yancin addini da ‘yancin yin ibada ga kowa da kowa, inda ya ce: “Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da kare waɗannan haƙƙoƙi na tsarin mulki kuma ta tabbatar da daidaito ga kowa a ƙarƙashin doka.”

Dangane da matakan da aka ɗauka wajen magance rashin tsaro, Idris ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙarfafa ayyukan haɗin gwiwar soji da ‘yan sanda a dukkan yankunan da abin ya shafa.

Ya bayyana cewa ayyukan da ake yi na yaki da ta’addanci sun rage ƙarfin ƙungiyoyin 'yan bindiga, sun tarwatsa hanyoyin satar mutane, sannan sun kai ga kama da kuma kawar da manyan ‘yan ta’adda.

Ministan ya ce an ƙara inganta musayar bayanai da haɗin gwiwar hukumomi don inganta tsarin gargaɗi da saurin mayar da martani, musamman a al’ummomin karkara masu rauni.

Haka kuma, ministan ya ce an ƙara sa ido da tsabtace dazuzzuka waɗanda ƙungiyoyin masu aikata laifi suka daɗe suna amfani da su, inda aka horar da jami’an tsaron daji na musamman don hana ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga samun mafaka, inganta ikon yankin, da ƙarfafa tsaro a matakin al’umma.

Ya ƙara da cewa waɗannan matakai na samun tallafi ne daga ƙarin zuba jari a kayan aiki, motoci, da fasaha ga sojoji da sauran hukumomin tsaro.

Bugu da ƙari, ministan ya ce an ci gaba da inganta tallafin jin ƙai ga ‘yan gudun hijira na cikin gida, sauƙaƙe dawo da al’ummomin da abin ya shafa lafiya, da kuma tallafawa shirye-shiryen gina zaman lafiya a matakin al’umma don samar da zaman tare mai ɗorewa.

No comments