Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur a matakin gantry da N25 kan kowace lita, inda farashin ya sauko daga N799 z...
Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur a matakin gantry da N25 kan kowace lita, inda farashin ya sauko daga N799 zuwa N774 kan kowace lita.
Sanarwar, wadda Sashen Ayyukan Kasuwanci na Dangote FZE ya aikawa masu kasuwancin mai, ta tabbatar da cewa sabon farashin zai fara aiki nan take.
A cikin takardar da aka aike wa ‘yan kasuwa, kamfanin ya ce: “Ana sanar da ku cewa an sauya farashin fetur na gantry daga N799 zuwa N774 kan lita.”
Matatar ta kuma bayyana cewa shirin tallafin ɗaukar kaya (lifting incentive) da take bai wa masu kasuwanci ya zo ƙarshe, tana mai nuni da cewa wannan sabon gyaran farashi zai ƙara inganta gasa tsakanin kayayyakin da ake tacewa a cikin gida.
Rage farashin na ranar Talata shi ne sabon sauyi a farashin wannan muhimmin kaya, wanda masana ke cewa yana da alaƙa kai tsaye da canjin darajar naira da kuma farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.

No comments