Jihar Neja ta cika shekara 50 da kafuwa a ranar Talata, inda aka yi kiran a sabunta ƙudirin haɗin kai da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa domi...
Jihar Neja ta cika shekara 50 da kafuwa a ranar Talata, inda aka yi kiran a sabunta ƙudirin haɗin kai da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa domin gina makoma mai ƙarfi ga jihar.A cikin wata sanarwa da ya fitar ta taya murna a ranar Talata, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa wannan biki shaida ce ta juriya, sadaukarwa, da ɗorewar fata ta mutanen jihar waɗanda suka himmatu wajen samun ci gaba.
Idris, wanda ɗan asalin Neja ne, ya ce bikin ba wai na tunawa da wucewar shekarun da suka shuɗe kawai ba ne, dama ce ta waiwayen tafiyar da mutanen Jihar Neja suka yi, nasarorin da aka samu, ƙalubalen da aka fuskanta, da kuma alƙawarin neman kyakkyawar makoma da ke gaba.
Ministan ya tunatar da cewa an ƙirƙiri Jihar Neja ne a cikin 1976 tare da jihohin Imo, Binuwai, Ogun, Ondo da Osun, kuma tun daga sannan ta samu matsayi na musamman a tarihin Nijeriya.
Ya bayyana cewa a matsayin ta na jiha mafi girma a ƙasar nan ta fuskar faɗin ƙasa, tare da bayar da gagarumar gudunmawa da take yi ga Gundumar Babban Birnin Tarayya (FCT), Jihar Neja na da yalwar ƙasa mai amfani ga noma da kuma muhimman albarkatu.
A cewar sa, jihar wata matattarar muhimman madatsun ruwa ce wadda ke samar da lantarki kamar dam ɗin Kainji, Jebba da Shiroro, waɗanda ke taka rawar gani wajen cigaban Nijeriya ta hanyar bai wa masana’antu wuta, tallafa wa noma, da kuma samar da hanyoyin dogaro da kai a faɗin ƙasar nan.
Yayin da ya amince cewa Jihar Neja, kamar sauran jihohi, ta ɗore a tafarkin mulkin dimokiraɗiyya duk da sauye-sauyen zamani, Ministan ya jaddada cewa ya kamata bikin ya zama wata dama ta tsara kyakkyawar hanya zuwa ga cigaba mai haɗa kowa da kowa da sauyi mai ɗorewa.
Ya ce rarraba jihar zuwa yankunan Neja ta Gabas, Neja ta Arewa da Neja ta Kudu ya ƙara jaddada muhimmancin haɗin kai, shugabanci nagari, haɗewar al’adu, da kuma manufofi masu ma’ana.
Idris ya ce tafiyar gina Jihar Neja mai cikakken haɗin kai da wadata yana ci gaba da gudana, inda ya ƙara da cewa a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ana aiwatar da tsare-tsare na farfaɗo da tattalin arziki a faɗin ƙasa, inda Jihar Neja ke ci gaba da cin gajiyar shirye-shiryen bunƙasa tattalin arziki, sabunta ababen more rayuwa, da gyaran cibiyoyi.
Ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su fuskanci halin da ake ciki a yanzu, su ƙarfafa cibiyoyi, sannan su himmatu wajen samar da shugabanci mai amfani ga jama'a.
Ya kuma jaddada muhimmancin karrama waɗanda suka kafa Jihar Neja da sauran masu kishin ƙasa da suka shimfiɗa tubalin dimokiraɗiyya shekaru 50 da suka gabata.
A cewar Ministan, Jihar Neja tana kan wani muhimmin mataki yayin da ta kai shekara 50, inda ta hanyar rungumar wannan labari na bai ɗaya na fata, sanin ya-kamata da haɗin kai, za a iya sabunta ƙudiri na gina makomar da za ta cika burin al’ummar jihar.
Ya yi kira ga al’ummar Jihar Neja da su ba Gwamnan Jihar, Umaru Mohammed Bago, cikakken goyon bayan da yake buƙata wajen ciyar da jihar gaba.
No comments