Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Shirin Horar Da ’Yan Nijeriya Miliyan 10 Kan Hada-hadar Kuɗi

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da shirin horas da ’yan ƙasa miliyan 10 kyauta kan ilimin hada-hadar kuɗi da shigar kuɗi cikin tsari...


Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da shirin horas da ’yan ƙasa miliyan 10 kyauta kan ilimin hada-hadar kuɗi da shigar kuɗi cikin tsari, inda ta ce matasa da mata ne ginshiƙin cin gajiyar yawan al’ummar kasar. 

Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana hakan a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, yayin da yake wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ya ce ba za a iya gina tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya ba tare da ƙwararrun ma’aikata, nagartattun ƙa’idoji da ingantaccen tsarin sana’o’i ba.

A yayin taron, Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa ta hannun Kwamitin Shugaban Kasa kan Hada-hadar Kuɗi da Tattalin Arziki (PreCEFI) ya rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimta (MoU) da manyan ƙungiyoyin ƙwararru shida da suka hada da ICAN, CIBN, CIS, NICA, CRMI da NIIE. 

Yarjejeniyar na da nufin tsara horo, bada takardar shaidar kwarewa, amfani da fasahar zamani da tsarin tallafi domin karfafa gwiwar ’yan kasuwa, musamman mata da matasa. Shettima ya ce hada-hadar kudi ba ta tsaya ga samun dama kadai ba, sai an samu ilimi, kwarewa da amana.

Shugaban ICAN, Mallam Haruna Nma Yahaya, ya yabawa gwamnatin Tinubu bisa gyare-gyaren tattalin arziki da suka haifar da kaddamar da shirin. Ya tabbatar da cikakken goyon bayan kungiyoyin kwararru wajen ganin an cimma nasarar shirin. 

Haka nan, Shugaban WAWU Africa, Emmanuel Lennox, ya ce sun shirya samar da dandamalin zamani da kayan aiki da za su tabbatar da ingancin horon. An bayyana cewa shirin na da muhimmanci domin rage ficewar jama’a daga tsarin hada-hadar kudi sakamakon karancin ilimi da kwarewa.




 

No comments