Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hukumar Shari’a Ta Kano Ta Haramta Rufe Tituna Yayin Sallar Juma’a

Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta bayar da umarni ga dukkan masallatan Juma’a a faɗin jihar da su dakatar da rufe hanyoyin jama’a yayin gudan...



Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta bayar da umarni ga dukkan masallatan Juma’a a faɗin jihar da su dakatar da rufe hanyoyin jama’a yayin gudanar da sallar Juma’a, tana mai cewa matakin ya zama wajibi domin kare zaman lafiya da kuma haƙƙin masu amfani da hanya.

A wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta jaddada cewa ko da yake sallar Juma’a ibada ce mai muhimmanci a addinin Musulunci, dole ne a gudanar da ita cikin tsari da ladabi ba tare da hana zirga-zirga ko jefa rayuka cikin haɗari ba. 

Hukumar ta ce, duk masallacin da aka samu da karya wannan umarni zai fuskanci hukunci a gaban kotu.

Matakin na zuwa ne bayan korafe-korafe da suka daɗe suna tashi daga mazauna gari da direbobi kan yadda ake rufe manyan tituna a lokacin sallar Juma’a, lamarin da ke haddasa cunkoso da toshe hanyoyin wucewa, musamman a muhimman sassan birnin Kano.

Masu lura da al’amuran zamantakewa na ganin cewa wannan umarni zai taimaka wajen samar da daidaito tsakanin ‘yancin gudanar da ibada da kuma buƙatar kiyaye walwalar jama’a da zirga-zirga. Sai dai wasu na ganin cewa ya kamata gwamnati ta ƙara faɗaɗa masallatai ko samar da tsare-tsare na musamman domin magance matsalar cunkoso a lokutan ibada.

A halin yanzu, ana sa ran jami’an tsaro da hukumomin da abin ya shafa za su fara sanya ido domin tabbatar da aiwatar da wannan umarni a faɗin jihar.

No comments