Gwamnatin Tarayya ta amince da sake buɗe iyakar ƙasa ta Tsamiya da ke Jihar Kebbi domin gudanar da cinikayya, tare da tsauraran matakan ts...
Gwamnatin Tarayya ta amince da sake buɗe iyakar ƙasa ta Tsamiya da ke Jihar Kebbi domin gudanar da cinikayya, tare da tsauraran matakan tsaro da bin doka.
Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Nijeriya, CG Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a Kebbi, ciki har da ’yan kasuwa, masu safarar kaya da ’yan kasuwar albasa.
Adeniyi ya ce gwamnati ba ta yi kunnen uwar shegu da halin ƙuncin da aka shiga sakamakon rufe iyakokin ba, inda ya jaddada cewa an shafe lokaci ana tattaunawa a matakin diflomasiyya, tsaro da kwastam da maƙwabtan ƙasashen. Ya bayyana cewa an karɓi wata tawaga ta gaggawa daga Hukumar Kwastam da Ƙungiyar Kasuwanci ta Jamhuriyar Nijar a Abuja, domin gaggauta warware cikas ɗin cinikayya.
“Ina farin cikin sanar da amincewar Shugaban Ƙasa cewa za a sake buɗe iyakar Tsamiya don ayyukan kasuwanci,” in ji shi.
Shugaban Kwastam ɗin ya yi gargaɗin cewa buɗewar za ta gudana ne karkashin tsauraran ƙa’idojin tsaro, domin hana miyagu cin gajiyar hanyoyin kasuwanci. Ya ce za a yi amfani da fasahar ICT wajen haɗa bayanan kwastam da na Nijar da Benin, tare da sa ido kan zirga-zirgar kaya. Ya kuma gargadi masu safara da kada su karkatar da kaya daga hanyar da aka amince da ita, yana mai cewa duk motar da aka kama za a ƙwace ta, tare da ɗaukar matakin shari’a.
Adeniyi ya ƙara da cewa bunƙasa al’ummomin da ke rayuwa a iyaka na da muhimmanci wajen tabbatar da tsaro da haɗin kai.

No comments