Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam Ta Duniya Ta Nemi A Binciki Zargin El-Ruaf'i Kan Batan Dadiyata

Daga Ibrahim Muhammad, Kano  An yi kira ga hukumomi a ƙasar nan da su zurfafa bincike kan ɓatan Dadiyata domin gano gaskiyar lamarin. Ƙungiy...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano 

An yi kira ga hukumomi a ƙasar nan da su zurfafa bincike kan ɓatan Dadiyata domin gano gaskiyar lamarin.

Ƙungiyar kare haƙƙin Ɗan Adam ta 'Amnesty International' ne ta yi wannan, inda ta yi nuni da cewa zargin da Malam Nasir El-Rufai ya yi cewa gwamnatin tsohon Gwamnan Kano, Daktar Abdullahi Umar Ganduje na da masaniya game da ɓatan Dadiyata, abu ne mai girma da ke buƙatar cikakken bincike da bin ƙwaƙƙwafi.

Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa shi bai san inda Dadiyata yake ba, kasancewar Dadiyata na adawa da Gwamnatin Ganduje, kasancewar sa ɗan Kwankwasiyya  a lokacin mulkin Ganduje ne aka je gidan sa da ke Kaduna aka kuma ɗauke shi.

Sai dai tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na gwamnatin Ganduje, Muhammad Garba ya musanta wannan zargin, inda ya ce babu ƙanshin gaskiya a cikin zargin.

Daga na shi ma ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Tun a ranar 2 ga Agusta a shekarar  2019 ne aka je gidan Dadiyata da ke Kaduna aka ɗauke shi, wanda kuma tun daga lokacin har zuwa yanzu  babu labarin a inda yake.
 

No comments