Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

EFCC Ta Tsare El-rufai Kan Binciken Biliyan N432, Yayin Da Yake Fuskantar Sabbin Tuhume-tuhumen DSS

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya (EFCC) ta tsare tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a daren Litinin a hedikwatar t...



Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya (EFCC) ta tsare tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a daren Litinin a hedikwatar ta da ke Jabi, Abuja, bayan shafe sa’o’i ana yi masa tambayoyi kan zargin badaƙalar kuɗi har Naira biliyan 432.

Majiyoyi daga cikin hukumar sun shaida cewa El-Rufai ya isa ofishin EFCC da misalin ƙarfe 10 na safe domin amsa gayyata, amma har zuwa ƙarshen daren Litinin yana hannun jami’an bincike.

Wani babban jami’in EFCC ya ce: “Har yanzu yana tsare, kuma ba za a sake shi yau ba.”

Binciken Majalisar Dokokin Kaduna:

Ana binciken tsohon gwamnan ne sakamakon rahoton da Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta fitar a 2024, wanda ya zargi gwamnatinsa da karkatar da lamuni, karya ƙa’idojin bayar da kwangila, da jefa jihar cikin ɗimbin bashi tsakanin 2015 da 2023.

Rahoton ya samo asali ne daga kwamitin wucin gadi da majalisar ta kafa domin duba harkokin kuɗi a lokacin mulkinsa. Shugaban kwamitin, Henry Zacharia, ya zargi cewa yawancin lamunin da aka karɓo ba a yi amfani da su bisa manufar da aka ce za a yi ba.

Kakakin majalisar, Yusuf Dahiru Leman, ya shaida wa ‘yan majalisa cewa kusan Naira biliyan 423 an wawure su, lamarin da ya bar jihar cikin nauyin bashi mai yawa.

Kwamitin ya ba da shawarar a gurfanar da tsohon gwamnan da wasu manyan jami’an gwamnatinsa kan zargin cin zarafin ofis, rashin bin ƙa’ida wajen bayar da kwangila, wanke kuɗi, karɓar lamuni ba tare da tsari ba, da kuma karkatar da kuɗaɗen jama’a. An aika koke ga EFCC da kuma Hukumar ICPC.

Daga cikin zarge-zargen da aka lissafo har da batun biyan kuɗaɗe da kwangiloli da suka haura Naira miliyan 155, zargin karkatar da Naira biliyan 1.37 da aka ware domin aikin layin dogo na birnin Kaduna, da kuma zargin wanke Naira miliyan 64.8 da wasu manyan hadimansa suka yi.

Sai dai El-Rufai ya musanta dukkan zarge-zargen, yana mai cewa siyasa ce ta haifar da su, kuma duk lamunin da aka karɓo an yi amfani da su ne bisa doka wajen ayyukan more rayuwa, ilimi, lafiya da tsaro.

Sabbin tuhume-tuhume a kotu:

A wani sabon salo kuma, Gwamnatin Tarayya ta shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin kutse cikin sadarwar wayar Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.

Ana zargin cewa kalaman da El-Rufai ya yi a wani shiri na Prime Time a tashar Arise TV sun nuna cewa shi da wasu abokan hulɗarsa sun samu damar sauraron wata tattaunawa da aka ce ta fito daga wayar NSA.

Takardun kotu sun ce a hirar da aka yi da shi ranar 13 ga Fabrairu, 2026, ya amsa cewa shi da “abokan aikinsa” sun kutsa cikin sadarwar ba bisa ƙa’ida ba.

Ana kuma zarginsa da sanin mutumin da ya aikata wannan laifi ba tare da kai rahotonsa ga hukumomi ba, da kuma amfani da na’urorin fasaha da suka jefa tsaron ƙasa cikin haɗari.

Har yanzu ba a sanya ranar gurfanar da shi a kotu ba.

DSS ta sake buɗe bincike kan ɓacewar Dadiyata:

A gefe guda, Hukumar Tsaro ta DSS ta sake buɗe bincike kan ɓacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.

Dadiyata, malami a Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma a Jihar Katsina, ya ɓace ne tun ranar 1 ga Agusta, 2019, bayan wasu ‘yan bindiga sun sace shi daga gidansa a Kaduna. Har yanzu ba a san inda yake ba.

Majiyoyin tsaro sun ce DSS ta ƙwace fasfon El-Rufai a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport domin hana shi fita daga ƙasar yayin da bincike ke gudana.

Ana kuma binciken wasu saƙonni da ‘ya’yansa suka wallafa a kafafen sada zumunta bayan ɓacewar Dadiyata, duba da zargin cewa malamin ya kasance mai sukar gwamnati a fili.

Sai dai El-Rufai ya musanta hannu ko sani a lamarin ɓacewar Dadiyata, yana mai cewa bai taɓa sanin malamin kai tsaye ba kuma ba shi da wani dalilin da zai sa a kai masa hari.

No comments