Wannan wata takardar kotu da Jaridar MATATTARAR LABARAI ta ci karo da ita, wacce Gwamnatin Tarayya ke zargin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna...
Wannan wata takardar kotu da Jaridar MATATTARAR LABARAI ta ci karo da ita, wacce Gwamnatin Tarayya ke zargin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufai bisa kutse a waya.
An shigar da ƙara a gaban kotu kan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bisa zargin aikata laifuffuka da suka shafi kutse a hanyoyin sadarwa da kuma barazana ga tsaron ƙasa.
A cikin takardar tuhumar da aka shigar tsakanin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a matsayin mai ƙara da El-Rufai, mai shekaru 65, a matsayin wanda ake ƙara, ana zargin sa da aikata laifuffuka uku kamar haka:
Zargi na Farko:
Ana zargin cewa a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, yayin da ya ke tattaunawa a shirin Prime Time na tashar Arise TV a Abuja, El-Rufai ya amsa a hirar cewa shi da wasu abokan aikin sa sun yi kutse ba bisa ƙa’ida ba cikin sadarwar wayar Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.
Ana cewa wannan ya saɓa wa Sashe na 12(1) na Dokar Hana Laifukan Yanar Gizo ta 2024 (Cybercrimes Act Amendment 2024), wadda ta tanadi hukunci kan duk wanda ya kutsa ko ya sa a kutsa cikin hanyoyin sadarwa ba tare da izini ba.
Zargi na Biyu:
A zargi na biyu, ana tuhumar El-Rufai da bayyana cewa yana da alaƙa da wani mutum da ya aikata wannan kutse cikin wayar NSA, amma bai kai rahoton lamarin ga hukumomin tsaro da abin ya shafa ba.
Ana cewa hakan ya saɓa wa tanade-tanaden dokar da ta haramta ɓoye ko rashin kai rahoton aikata laifi ga hukumomin da suka dace.
Zargi na Uku:
Zargi na uku ya ce a shekarar 2026, a Abuja, El-Rufai tare da wasu da suka arce, ba a kama su, sun yi amfani da na’urori ko fasahohin sadarwa ta yadda suka jefa tsaron jama’a da na ƙasa cikin haɗari, tare da haifar da fargabar rashin tsaro a tsakanin ‘yan Nijeriya, ta hanyar yin kutse cikin sadarwar wayar NSA.
Ana danganta wannan zargi da karya Sashe na 131(2) na Dokar Sadarwa ta Nijeriya ta 2003 (Nigerian Communications Act 2003).
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu cikakken bayani daga ɓangaren El-Rufai kan tuhumar da ake masa. Haka kuma, kotu ba ta bayyana ranar fara sauraron ƙarar a hukumance ba.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da batutuwan tsaro da kare sirrin hanyoyin sadarwa ke ci gaba da zama muhimman batutuwa a Nijeriya.

No comments