Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Mataimakin sa, Kashim Shettima, da ya jagoranci wata babbar tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Jihar...
Ana sa ran tawagar za ta tashi daga Abuja yau domin isar da saƙon ta’aziyyar Shugaban Ƙasa ga ‘yan kasuwar da suka yi asarar dukiyoyi na biliyoyin Naira sakamakon gobarar da ta tashi a ƙarshen mako, lamarin da ya zama na biyu cikin makonni biyu.
Haka kuma, tawagar za ta bayar da tallafin kuɗi ga waɗanda abin ya shafa tare da tallafa wa gwamnatin jihar wajen hanzarta sake buɗe kasuwar domin ci gaba da harkokin kasuwanci.
Cikin tawagar akwai Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin; Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila; da Hon. Abubakar Kabir Bichi.
Sauran mambobin tawagar sun haɗa da Ministan Harkokin Jin-ƙai, Dakta Bernard M. Doro, da Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (National Emergency Management Agency), Misis Zubaida Umar.
Tun da farko, Shugaba Tinubu ya tattauna ta wayar tarho da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya jajanta masa da al’ummar jihar bisa wannan mummunan ibtila’i.
Gobarar wadda ta tashi a yammacin ranar Asabar ta ci gaba da ƙone kasuwar har zuwa safiyar Lahadi, inda ta lalata dukiyoyi masu tarin yawa a babbar kasuwar abinci mafi girma a Najeriya.
Shugaban Ƙasar ya kuma nuna damuwarsa matuƙa kasancewar wannan shi ne karo na biyu da gobara ta tashi a kasuwar cikin ƙasa da makonni biyu, inda ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin yawaitar gobarar kasuwanni da ke jefa ‘yan kasuwa cikin mawuyacin hali.

No comments