Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Kaddamar Da Raron Manyan Tiransfoma 600 Da Fitilun Tituna Na Solar 10,000

Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Kaduna tare da haɗin gwiwar Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kaduna sun ƙaddamar da rarraba manyan t...


Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Kaduna tare da haɗin gwiwar Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kaduna sun ƙaddamar da rarraba manyan tiransfoma 600 da fitilun tituna na hasken rana (solar) 10,000 ga dukkanin kananan hukumomi 23 na jihar. An gudanar da bikin kaddamarwar a Fadar Gwamnati da ke Sir Kashim Ibrahim House, Kaduna, inda manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta.

A jawabinsa  Kwamishinan Kananan Hukumomi,  Sadiq Mamman Lagos, ya bayyana muhimmancin shirin, yana mai cewa wannan haɗin gwiwa ne domin tabbatar da shugabanci mai haɗa kai da kuma bunƙasa yankunan karkara da waɗanda ba su da isassun kayayyakin more rayuwa. 

Ya kuma bukaci shugabannin kananan hukumomi, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da su ɗauki nauyin kula da kayayyakin da aka raba tare da kare su daga ɓarna.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya jaddada cewa wannan shiri wani mataki ne na zahiri domin inganta rayuwar al’ummar jihar. 

Akan hakan ya yaba da kokarin shugabannin kananan hukumomi 23 wajen ganin an aiwatar da shirin cikin nasara, yana mai cewa hakan na nuna ƙudurin gwamnati na samar da muhimman ayyuka da hidimomi ga al’umma a fadin jihar.

Taron ya nuna aniyar Gwamnatin Jihar Kaduna na magance ƙalubalen da al’umma ke fuskanta tare da tabbatar da shugabanci nagari, gaskiya da rikon amana.

 

No comments