Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya dawo da shirin ɗaukar nauyin Kiristoci zuwa ziyarar ibada a Jerusalam na Isra'ila, wanda gwamnatin jih...
Shugabar Ma’aikata ta gwamnatin jihar Kaduna, Jimami C. Bako, ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi a wurin taron bitar shekarar 2025 ga maniyyata Kiristoci 50 da gwamnati ta ɗauki nauyi.
Taron bitar ya nuna karon farko da jihar ta ɗauki nauyin sauke farali na Kiristoci cikin fiye da shekara 11 da dakatar da shi da gwamnatocin baya suka yi.
Shugabar ma’aikatan ta jihar Kaduna ta yaba wa Gwamna Uba Sani bisa dawo da shirin na daukar nauyin sauke faralin Kiristoci.
Jimami C. Bako ta bayyana cewa gwamnatin ta amince da cewa bunƙasar ayyukan ibada da kyawawan ɗabi’u muhimman abubuwa ne da ke tafiya tare da samar da ababen more rayuwa da ci gaban tattalin arziki.
Ta ƙara da cewa, farfaɗo da shirin sauke faralin ya nuna irin salon shugabanci ne da ke ɗaukar addini a matsayin ginshikin zaman lafiya da haɗin kan al’umma.
Kwamishinan yaɗa labarai, Ahmed Maiyaki, ya bayyana cewa wannan matakin ya yi daidai da ƙudurin gwamnatin na samar da adalci, daidaito, da kuma tafiya tare da kowa da kowa ba tare da la’akari da addini ba.
Kwamishinan ya buƙaci maniyyatan da su yi amfani da wannan dama su yi addu’ar neman zaman lafiya, haɗin kai, da dorewar arziki a jiha da ma kasa baki ɗaya.
Ga waɗanda suka amfana, dawo da shirin sauke faralin ya zama alama ta sabon fata, karfafa amincewa ga gwamnatin jiha, da kuma karfafa zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban a Kaduna.
A watan Nuwamba na shekarar 2014, maniyyata Kiristoci 567 daga Kaduna ne aka kwashe daga filin jirgin saman jihar zuwa kasar Isra’ila.
Yayin da yake jawabi a filin jirgin saman lokacin da suke tashi, Ramalan Yero, wanda shi ne gwamnan jihar a lokacin, ya buƙaci maniyyatan da su kasance jakadu nagari na Nijeriya yayin da suke a Isra’ila.

No comments