Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

El-Rufai Ya Nemi Kotu Ta Dakatar da ICPC, EFCC da DSS Daga Ƙwace Kadarorin Sa

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya roƙi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta hana hukumomin yaƙi da cin hanci da kuma DSS ɗau...


Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya roƙi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta hana hukumomin yaƙi da cin hanci da kuma DSS ɗaukar duk wani mataki na toshe asusun ajiyar sa ko ƙwace kadarorin sa.

A cikin wata sabuwar ƙarar da lauyan sa, Oluwole Iyamu (SAN), ya shigar, El-Rufai ya nemi umarnin wucin-gadi da zai tilasta wa waɗanda ake ƙara su ci gaba da kiyaye halin da ake ciki kafin a kammala sauraron ƙarar.

Ya ce wannan mataki ya zama dole domin kauce wa abin da doka ta kira fait accompli — wato aiwatar da abu kafin kotu ta yanke hukunci.

Hukumomin da ya sanya cikin ƙarar sun haɗa da ICPC a matsayin wanda ake ƙara na farko, sai EFCC, DSS da kuma Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a a matsayin wanda ake ƙara na huɗu.

A cikin takardun shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/368/2026, tsohon gwamnan ya nemi kotu ta ayyana cewa kuɗin sallamarsa da ya karɓa bayan kammala wa’adin sa daga 2015 zuwa 2023 ba za a iya zargin su a matsayin kuɗaɗen haramtacciyar hanya ba. Ya ce kuɗin sun samo asali ne daga tanade-tanaden doka, ciki har da Dokar Fansho da Giratuti ta Gwamna da Mataimakinsa ta 2006 (wadda aka yi wa gyara a 2013 da 2020), da kuma ƙa’idojin Hukumar RMAFC.

El-Rufai ya jaddada cewa duk kadarorin da ya saya da waɗannan kuɗaɗe mallakarsa ce bisa doka. Haka kuma ya bayyana wasu asusun ajiyar sa da ke Zenith Bank Plc, Guaranty Trust Bank Plc da kuma Access Bank Plc, yana mai neman kotu ta kare su daga duk wani umarni na wucin-gadi ko na ƙarshe da zai iya tauye haƙƙinsa ba tare da hujja mai ƙarfi ba.

Ya kuma nemi kotu ta ayyana cewa duk wani yunƙuri na neman umarnin kwace kadarori ta hanyar buƙatar ex parte ba tare da bayyana muhimman bayanai ba, zai zama saɓawa sashe na 36(5) na Kundin Tsarin Mulki wanda ke ba da kariya ga zato na rashin laifi da kuma haƙƙin sauraro adalci.

Bugu da ƙari, tsohon gwamnan ya nemi a ba shi diyya ta naira biliyan ɗaya a matsayin diyya ta gama-gari da ta misali bisa abin da ya kira barazanar tauye masa haƙƙinsa da kuma ɓata masa suna. Haka kuma ya nemi naira miliyan 100 a matsayin kuɗin shari’a.

A cikin hujjojinsa, El-Rufai ya ce bai taɓa samun hukuncin laifi a kansa ba, kuma a shirye yake ya ba da haɗin kai ga duk wani bincike da za a gudanar bisa ƙa’ida. Ya ce matakin da ya ɗauka na zuwa kotu ya samo asali ne daga buƙatar kare haƙƙinsa kafin a aiwatar da duk wani abu da zai iya zama tauye masa doka.

No comments