Bayan kusan shekaru uku cikin ruɗani, zarge-zarge da muhawara mai zafi a faɗin ƙasa, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta miƙa Walida Abdulh...
Bayan kusan shekaru uku cikin ruɗani, zarge-zarge da muhawara mai zafi a faɗin ƙasa, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta miƙa Walida Abdulhadi Ibrahim, wata matashiya da ake zargin jami'in DSS ya sace sannan ya ɗirka mata ciki ga gwamnatin jihar Jigawa.
A daren Laraba ne gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya karbi Walida a hedikwatar DSS da ke Abuja da misalin ƙarfe 10:40 na dare, bayan makonni na matsin lamba daga ƙungiyoyin farar hula da kuma sa ido daga jama’a.
Da yake jawabi bayan karbar, Gwamna Namadi ya bayyana Walida a matsayin “’yar jihar Jigawa,” yana mai ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta tabbatar da tsaron lafiyarta da kuma kula da duk wata damuwa ko raɗaɗin da ta fuskanta a tsawon lokacin da ta vace.
Ya ce, batun zai kasance a gaban kotu, yana mai jaddada cewa al’amari ne na jiha kuma za a tafiyar da shi bisa doka. Sai dai ya fayyace cewa karbar Walida a hannun jiha ba yana nufin nan take za a mayar da ita Jigawa ba, domin za a tsare ta a Abuja na ɗan lokaci tare da samar mata da cikakken tsaro.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa jaririyar da Walida ta haifa a watan Nuwamban 2025 za ta kasance ƙarƙashin kulawar gwamnatin Jigawa har sai kotu ta yanke hukunci kan batutuwan da suka taso.
Babban Daraktan DSS, Adeola Oluwatosin Ajayi, ne ya jagoranci miƙa Walida tare da manyan jami’an hukumar. Wakilai daga Majalisar Kula da Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA), Ƙungiyar Lauyoyi Mata ta Ƙasa (FIDA), da sauran ƙungiyoyin farar hula sun halarci taron, tare da manema labarai. Sai dai iyayen Walida ba su halarta ba, lamarin da ya janyo tambayoyi daga jama’a.
Walida ta vace ne a shekarar 2023 daga ƙaramar hukumar Hadejia a Jigawa. Rahotanni sun nuna cewa an fara zargin wata mata mai suna Mariam da sace ta tare da cin zarafinta, kafin daga bisani ta bace. Daga baya ta bayyana a Abuja inda aka ce ta zauna tare da wani jami’in DSS, Ifeanyi Onyewuenyi, wanda har yanzu ke tsare yayin da ake ci gaba da bincike.
Lamarin ya sake ɗaukar sabon salo bayan wata hira da aka wallafa a ranar 21 ga Fabrairu 2026, inda Walida ta bayyana abubuwan da ta fuskanta. Hakan ya tayar da qura a tsakanin ƙungiyoyin addini da na kare haqqin bil’adama, ciki har da Ƙungiyar Kare Muradun Musulmi ta MURIC, waɗanda suka nemi a miƙa ta ga kulawa mai zaman kanta.
Daraktan DSS ya kare matakan da hukumar ta ɗauka, yana mai cewa manufar su ita ce tabbatar da tsaron Walida da makomarta. Ya bayyana cewa binciken ya haɗa da hukumomi da dama, ciki har da ‘yan sanda, Civil Defence, FIDA da Ma’aikatar Mata ta Tarayya. Har ila yau, an gayyaci ƙungiyar likitoci ta ƙasa domin tantance lafiyar kwakwalwarta.
Ajayi ya yi gargaɗi kan haɗarin ɗora batun kan rikicin addini ko ƙabilanci, yana tunatar da irin rikicin da ya taba tasowa a shari’ar Ese Oruru a Bayelsa.

No comments