Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

CREDICORP: Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Hukumar Kula Da Lamunin Jari da Ƙarfafa Kasuwanci

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a madadin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da kwamitin gudanarwa na Nigerian Consumer...


Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a madadin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da kwamitin gudanarwa na Nigerian Consumer Credit Corporation (CREDICORP).

Da yake jawabi a wajen taron, Shettima ya bayyana cewa samun lamunin na (consumer credit) na da matuƙar muhimmanci ga burin Najeriya na gina tattalin arziƙin da darajarsa za ta kai dala tiriliyan ɗaya. Ya ce ba za a iya inganta rayuwar ’yan ƙasa ba muddin akwai gibin samun jari da kuma mutuncin ɗan Adam.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ne ya kafa CREDICORP domin gina amintaccen tsarin bayar da bashi, samar da jari mai haɓɓaka kasuwa (catalytic capital) da zai rage tsadar lamuni, tare da taimaka wa ’yan Najeriya su shawo kan ɗabi’ar ƙin karɓar lamuni da ta daɗe a cikin al’umma.

A cewarsa, shirin zai taimaka wajen faɗaɗa damar samun kuɗaɗe ga jama’a, ƙarfafa kasuwanci, da haɓaka walwalar rayuwar al’umma, a wani ɓangare na manyan sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa.



 

No comments