Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dalilan Da Suka Sa Gwamnati Ta Tilasta Wa Masu POS Yin Rajista -Ministan Yaɗa Labarai

"Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa gwamnatin tarayya ta yi rajistar masu POS shi ne ƙara inganta tsaro ga ’yan ƙasa a faɗin ƙasar nan....


"Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa gwamnatin tarayya ta yi rajistar masu POS shi ne ƙara inganta tsaro ga ’yan ƙasa a faɗin ƙasar nan.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya yi wannan jawabi ne yayinda ya karbi bakuncin  Shugaban Hukumar Rijistar Kamfanoni ta Nijeriya (CAC), Hussaini Ishak Magaji, a ranar 4 ga Fabrairu, 2026, a Abuja.

Ministan ya ƙara da cewa, "Akwai lokuta da dama da aka sha aikata laifuka ta hanyar na’urorin POS ba tare da wata hanyar bin diddigin waɗanda suka aikata laifin ba.

Amma sakamakon rajistar waɗannan cibiyoyin hada-hadar kuɗi, yanzu idan aka aikata laifi da na’urar POS ana iya bin diddiginsa, domin Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni ta Nijeriya (CAC) na iya samar da bayanan takamaiman mai na'urar POS din.

Don haka, abin farin ciki ne ganin cewa yanzu anyi musu rajistar da kuma tattara bayanan waɗannan masu POS yadda ya kamata, ba wai don shigar da su cikin tsarin biyan haraji na ƙasa kaɗai ba, har ma don tabbatar da gina tsarin tattalin arziki mai tsari da tsaro."
 

No comments