Ranar Lahadin da ta gabata ne aka gudanar da zaben sabbin shugabannin Ƙungiyar ’Yan Asalin Jihar Zamfara mazauna Jihar Kaduna a wani zabe ma...
Ranar Lahadin da ta gabata ne aka gudanar da zaben sabbin shugabannin Ƙungiyar ’Yan Asalin Jihar Zamfara mazauna Jihar Kaduna a wani zabe mai cike da karsashi da lumana, wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali da mutunta ƙa’idoji. An gudanar da zaben ne a sakatariyar 'yan jarida, NUJ ta jihar Kaduna.
Zaben ya samu halartar mambobin ƙungiyar Zamfarawan na jihar Kaduna da dama, inda aka samu ƙuri’u 269 masu inganci daga cikin masu kaɗa ƙuri’a 406 da suka cancanta.
Da yake jawabi ga ‘yan jarida a wurin zaben, tsohon Mataimakin Sufeton Janar na ’Yan Sanda (DIG mai ritaya), Mamman Ibrahim Tsafe, ya bayyana zaben a matsayin nasara, sakamakon yadda aka gudanar da shi cikin lumana da tsari.
Ya yaba wa mambobin ƙungiyar bisa nuna kamun kai da kishi, haɗin kai, tare da shawartar sabbin shugabannin da su jagoranci al’umma cikin tsoron Allah, adalci da kuma kyautata mu’amala da al’ummomin da suke masauki a cikinsu a Kaduna.
Ita ma shugabar mata, Hajiya A’isha Asma’u Muhammad Gusau, ta buƙaci sabbin shugabannin ƙungiyar da su mayar da hankali wajen ƙarfafa haɗin kai, girmama doka da oda, da kuma kare martabar ƙungiyar a kowane lokaci. Ta ce ci gaban qungiyar zai dogara ne da yadda shugabanci zai kasance mai gaskiya da riƙon amana.
A nasa bangaren, shugaban kwamitin tsaro na zaben, Kanal Rabi’u Garba Yandoto (mai ritaya), ya nuna jin daɗinsa ga mambobin ƙungiyar bisa yadda suka gudanar da zaben cikin lumana. Ya buƙaci zababbun jami’an da za su yi wa’adin shekaru huɗu da su rungumi kowa ba tare da nuna wariya ba, tare da aiki domin ciyar da ‘yan Zamfara da ke zaune a Kaduna gaba.
Haka zalika, CSP Bala Muhammad Kaura mai ritaya ya ja kunnen sabbin shugabannin da su guji duk wani abu da zai iya raba kan al’ummar Zamfara. Ya bayyana zaben a matsayin abin koyi, la’akari da yadda masu kaɗa ƙuri’a suka nuna kamun kai da kishin ƙungiya.
A jawabinsa bayan nasarar zabe, sabon Shugaban Ƙungiyar, Alhaji Balarabe Garba, ya yi alƙawarin tafiyar da shugabancinsa bisa tsarin buɗe ƙofa, tare da haɗa kai da kowa a ciki.
Ya ce yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali alama ce ta cewa ‘yan Zamfara mazauna Kaduna sun ƙuduri aniyar ci gaba da zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya domin samun cigaba mai ɗorewa. Ya kuma tabbatar da cewa shugabancinsa zai kasance mai gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da dukiyar ƙungiyar.
Matar shugaban da aka zaba, Hajiya Jamila Abdullahi, ta bayyana mijinta a matsayin shugaba nagari mai gaskiya, tana mai cewa yana da ƙudurin ɗaukar ƙungiyar zuwa wani mataki mafi girma.
Daga cikin sauran zababbun jami’ai akwai Hajiya Asma’u Muhammad Shagamu Gusau a matsayin Jami’ar Walwala, Suleiman Rabi’u a matsayin Audita Janar, Aminu Isma’ila Kayayen Maru a matsayin PRO, Salisu Birnin Magaji a matsayin Sakataren Kuɗi, Sani Umar a matsayin Sakatare Janar, da sauran muƙamai.






No comments