Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kakkausar suka kan kisan gilla da aka yi wa wata matar aure, Fatima Abubakar, da ’ya’yanta shida a ung...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kakkausar suka kan kisan gilla da aka yi wa wata matar aure, Fatima Abubakar, da ’ya’yanta shida a unguwar Chiranci da ke Kano, inda ya bayyana lamarin a matsayin dabbanci da abin Allah-wadai.
A wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar a ranar Lahadi, Shugaban ya yaba wa rundunar ’yan sanda bisa gaggawar cafke manyan waɗanda ake zargi da aikata laifin, tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da su gaban kotu ba tare da jinkiri ba. Ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyar sa ga iyalan da abin ya shafa, yana mai addu’ar Allah Ya ji ƙan mamatan.
A cikin wannan sanarwar, Shugaba Tinubu ya kuma bayyana alhinin rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma jagoran al’ummar ’yan kasuwa a Jihar Kano, Alhaji (Dr) Bature Abdulaziz, wanda ya rasu a ƙarshen makon da ya gabata.
Shugaban ya ce rasuwar marigayin babbar asara ce, ba ga ’yan kasuwar Kano kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya, duba da irin tasirin da ya yi a harkokin kasuwanci da ƙungiyoyin ’yan kasuwa. Marigayi Dr Bature Abdulaziz ya kasance Shugaban ƙungiyar “Harmonised Traders Association of Nigeria”, tare da taka rawa a wasu ƙungiyoyin kasuwanci na ƙasa.
Tinubu ya kuma tuna irin gudunmawar da marigayin ya bayar a yaƙin neman zaben shekarar 2023, da kuma jajircewar sa wajen inganta haɗin kan ƙasa da kishin ƙasa ta hanyar “Patriotic Elders Network for Peace” (PENP) da ya assasa.
Shugaban ya miƙa sakon ta’aziyyar sa ga ’yan kasuwa a Kano, da jama’ar jihar baki daya, da kuma gwamnatin Jihar Kano, bisa wannan rashi

No comments