Rundunar ’Yan sanda ta jihar Kano ta samu nasarar kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa wata mata da ’ya’yanta s...
Rundunar ’Yan sanda ta jihar Kano ta samu nasarar kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa wata mata da ’ya’yanta shida a Unguwar Ɗorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano.
A cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Lahadin na ta bayyana cewa kamen ya biyo bayan wani a bayanin sirri, aka gudanar da aiki, wanda aka gudanar bisa umurnin Sufeto janar na ’Yan sanda, Kayode Egbetokun, tare da kulawar Kwamishinan ’Yan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori.
Kakakin rundunar ya ƙara da cewa an kama waɗanda ake zargin ne a wani samame da aka gudanar daga ƙarfe 10:00 na dare a ranar 17 ga Janairu zuwa ƙarfe 4:00 na asubahin ranar 18 ga Janairu, 2026.
Sanarwar ta bayyana waɗanda aka kama ɗin da cewa, sun haɗa da Umar Auwalu, mai shekaru 23 daga Unguwar Sabuwar Gandu; Isyaku Yakubu da aka fi sani da “Chebe”, mai shekaru 40 daga Unguwar Sagagi; da Yakubu Abdulaziz wanda aka fi kira da “Wawo”, mai shekaru 21 daga Unguwar Sabon Gida Sharada.
Rundunar ’Yan sandan ta bayyana cewa wanda ake zargi da jagorantar kisan, Umar Auwalu, wanda ɗan uwa ne ga marigayiyar, ya amsa laifin aikata kisan. Haka kuma, ya bayyana cewa sun aikata wasu kashe- kashe masu tada hankali a wasu sassan Kano a baya-bayan nan.
Daga cikin abubuwan da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin akwai tufafi masu tabon jini, wayoyin salula biyu na marigayiyar, adda, gora, kuɗi, waɗanda ake zargin an ƙwace a wajen da abin ya faru ne, da wasu makamai masu haɗari. Rundunar ta ce bincike na ci gaba.
Rundunar ’Yan sanda ta Jihar Kano ta yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da gode wa al’umma bisa addu’o’i, goyon baya da haɗin kai. Rundunar ta kuma tabbatar wa jama’a ƙudirinta na ganin an gurfanar da duk masu aikata laifuka a gaban ƙuliya.





No comments