Babban Mataimaki na musamman ga Shugaban Ƙasa akan Harkokin yaɗa labarai, Mal Abdul'aziz Abdul'aziz ya wakilci Shugaban ƙasa Asiwaju...
Babban Mataimaki na musamman ga Shugaban Ƙasa akan Harkokin yaɗa labarai, Mal Abdul'aziz Abdul'aziz ya wakilci Shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu GCFR wajen kai Ziyarar Ta’aziyya ga iyalan Mallam Haruna, wanda aka yi wa Matarsa da Ya'yansa guda 6 kisan gilla a Kano, inda ya yi masa ta,aziyya ya kuma tabbatar masa da cewa Shugaban ƙasa ya yi umarni da a tabbatar da an yi gaggawar yanke wa waɗanda su ka yi wannan mummunan aiki hukunci kamar yadda dokar ƙasa ta tanadar.
Daga nan kuma Malam Abdul'aziz ya kai wata ziyarar ta’aziyyar rasuwar ta Dr Abdulaziz Bature, wanda Allah ya yi wa rasuwa kwana uku da suka gabata, inda ya yi wa iyalai, 'yan uwa da Abokan arziki ta'aziyya a madadin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tunubu.
A ƙarshe ya yi addu'a Ubangiji ALLAH ta'ala ya ji ƙan su da rahama baki ɗaya.
No comments