Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar 'Dikko Na kowa Ne' Ta Jinjina Wa Gwamna Katsina Bisa Biyan Masu Ritaya Garatutin Biliyan 21

Daga Hussaini Yero, Funtua  Shugaban ƙungiyar 'Dikko Na kowane,' kuma Sakatare Ƙaramar Hukumar Funtuwa, Alhaji Hassan Musa Anda Funt...


Daga Hussaini Yero, Funtua 

Shugaban ƙungiyar 'Dikko Na kowane,' kuma Sakatare Ƙaramar Hukumar Funtuwa, Alhaji Hassan Musa Anda Funtua ya jinji wa gwamna Jihar Katsina Dr Umar Dikko Raɗɗa bisa biyan Ma'aikatan da suka yi ritaya haƙƙin su na sama da naira biyan Ashiri da Ɗaya ga Ma'aikatan Jihar da na Ƙananan Hukumomi da malamam Makarantar Firamare.

Hassan Musa ya kuma tabbatar da cewa, biyan waɗannan kuɗaɗe zai farfaɗo da tattalin arzikin Jihar Katsina, kuma zai taimaka gaya wajen ci gaban Jihar Katsina.

Ya ce, "Gwamna Umar Dikko Raɗɗa ya aje tarihi a Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya na biyan waɗannan bilyoyin nairori a lokaci guda, wannan kuma ya tabbatar wa Ma'aikatan Jihar Katsina cewa Dikko nasu ne mai jin ƙan su ne. Duk wanda Ritayar sa ta kusa, ba zai yi fargabar ajiye aikin ba, tunda yana ajiyewa, ana biyan sa haƙƙin sa."
 

No comments