Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jam'iyyar PDP A Zamfara Ta Yaba Wa Babbar Kotun Abuja Akan Nasarar Jam'iyyar

Daga Hussaini Yero Funtua, Gusau Jam'iyyar PDP reshen Jihar Zamfara ta yaba wa kotun tarayya da ke Abuja da ta yi masu adalci a hukuncin...


Daga Hussaini Yero Funtua, Gusau

Jam'iyyar PDP reshen Jihar Zamfara ta yaba wa kotun tarayya da ke Abuja da ta yi masu adalci a hukuncin da ta yanke a ranar Talata da ta gabata.

Shugaban riƙo na jihar, Hassan Daudawa ne ya yi wannan yabon a tattaunawar sa da manema labarai a hedikwatar Jamiyyar PDP da ke Gusau babban Birnin Jihar Zamfara.

Hassan Daudawa ya bayyana cewa nasarar ta ƙarfafa wa magoya bayan jam'iyyar gwiwa a dukkan matakai.

Sakamakon babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da Samuel Anyanwu ya shigar a ranar Talata, yana neman a tabbatar da shi a matsayin sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa.

Alƙalin kotun, Muhammed Umar, ya yi watsi da ƙarar bayan da lauyan Mista Anyanwu ya bayyana cewa wa'adin sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa ya ƙare a watan Disamba na 2025.

Waɗanda aka shigar da ƙara a matsayin waɗanda ake ƙara a cikin ƙarar sun haɗa da PDP, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Umar Damagun, shugaban jam'iyyar na ƙasa;  Sunday Udeh ‑ Okoye, Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP na ƙasa, Kudu maso Gabas; Ali Odela, mataimakin sakataren jam'iyyar na ƙasa; da Setonji Koshoedo, mataimakin sakataren jam'iyyar na ƙasa.

Daudawa ya ce "dukkan mu dole ne mu yi farin ciki da wannan nasara da za ta ƙarfafa tsarin gudanarwa na jam'iyyar mu, kuma jam'iyyar ta samu cikakiyar damar tsayawa takara a kowane mukami a babban zaben 2027 mai zuwa.

A cewar sa, dukkan Muƙaman cikin jam'iyyar, tun daga Kwamitin tsare-tsare na ƙasa (NWC), Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC), Kwamitin Amintattu, da Wakilai na ƙasa, duk suna nan daram.

Daudawa ya kuma taya hedikwatar jam'iyyar PDP ta ƙasa murna, tare da tabbatar da biyayyar su ga shugabancin Shugaban Jam'iyyar na ƙasa, Alhaji Kabiru Turaki wanda ya kasance shugaban jam'iyyar na ƙasa.

Akan haka ne Hassan Daudawa ya yi kira ga al'ummar ƙasar nan da su dawo ma Jam'iyyar gaskiya da gaskiya mai ƙaunar Jama'a da ci gaban al'umma, wato Jam'iyyar PDP don ceto su daga ƙangin da Jam'iyyar APC ta jefa su.
 

No comments