Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar da Sabbin Ayyukan Hanyoyi a Maƙarfi da Zariya

A ci gaba da ƙoƙarinsa na samar da ingantattun ababen more rayuwa a Jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani ya ƙaddamar da wasu manyan ayyukan hanyoyi...


A ci gaba da ƙoƙarinsa na samar da ingantattun ababen more rayuwa a Jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani ya ƙaddamar da wasu manyan ayyukan hanyoyi a Ƙananan Hukumomin Maƙarfi da Zariya, lamarin da ya kawo farin ciki da jin daɗi ga al’ummar yankunan.

Gwamnatin Jihar Kaduna, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani, ta kafa tarihi a fannin gine-ginen hanyoyi da ƙaddamar da titin Durum zuwa Kuruntumawa a Ƙaramar Hukumar Maƙarfi. Titin, wanda mazauna yankin ba su taɓa samun irinsa ba tsawon sama da shekaru goma, ana sa ran zai sauƙaƙa zirga-zirga da bunƙasa harkokin tattalin arziki a yankin.

Haka kuma, Gwamnan ya ƙaddamar da titin Magajiya zuwa Kasuwar Amaru da kuma titin Audi zuwa Kako a cikin birnin Zaria, ayyukan da ake ganin za su taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa tare da inganta harkokin kasuwanci da rayuwar al’umma.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da ayyukan, Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa gwamnatinsa ta biya sama da Naira biliyan ɗaya a matsayin diyya ga mutanen da gine-ginensu da kadarorinsu suka shiga cikin aikin titin Magajiya zuwa Kasuwar Amaru. Ya ce wannan mataki na da nufin tabbatar da adalci da kuma ganin an kammala aikin cikin nasara ba tare da wata matsala ba.

Gwamnan ya ƙara da cewa ayyukan hanyoyin da ake ƙaddamarwa wani ɓangare ne na manyan ayyuka guda 140 da gwamnatin ke aiwatarwa a faɗin jihar, waɗanda jimillarsu ta kai tsawon kilomita 1,335.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ta ɗauki gina ababen more rayuwa a matsayin ginshiƙi na ci gaba, tare da alƙawarin ci gaba da karkatar da akalar mulki zuwa ayyukan da za su inganta rayuwar al’umma, musamman a fannoni kamar sufuri, kasuwanci da walwalar jama’a.

Mazauna yankunan Makarfi da Zaria sun bayyana godiyarsu ga Gwamna Uba Sani, suna cewa waɗannan ayyuka za su kawo sauƙi ga zirga-zirga, rage wahalhalu, da kuma ƙarfafa cigaban tattalin arziki a yankunansu.

 

No comments