Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Binciken Shari’a Ya Sanya El-Rufai Gudun Hijira?

Rahotanni daga Jihar Kaduna na nuni da cewa tsohon Gwamnan jihar, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, ya yi batan-dabo a daidai lokacin da binciken...


Rahotanni daga Jihar Kaduna na nuni da cewa tsohon Gwamnan jihar, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, ya yi batan-dabo a daidai lokacin da binciken Majalisar Dokokin da kuma matakan shari’a ke ƙara zurfafa kan ayyukan gwamnatinsa na tsawon shekaru takwas.

A kwanan baya Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta gudanar da bincike kan mulkinsa, inda ta bayyana batutuwa da suka shafi manyan rance, kwangiloli da aiwatarwarsu, da kuma tsarin tafiyar da harkokin kuɗi.

Rahotonni Sun ruwaito cewa Sakamakon binciken ya sa aka tura rahoton zuwa hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa domin ƙarin bincike.

Sai dai Duk da cewa babu sanarwar gudun hijira a hukumance, amma tsawaita zamansa a ƙasashen waje ya jawo muhawara, inda wasu masu sharhi ke ganin tsohon gwamnan kamar ya guje wa yiwuwar fuskantar shari’a. Wannan hasashe ya ƙaru ne yayin da ake fara gurfanar da wasu daga cikin tsoffin mukarrabansa.

A wata muƙala da Masanin tattalin arziki da bunƙasar ci gaba daga Zariya, Malam ibrahim Jibril ya wallafa a wasu kafafen yaɗa labarai ya ce Masu kare El-Rufai dai na jaddada cewa bincike ba hukunci ba ne, kuma kotuna ne kaɗai ke da hurumin yanke hukunci. Sai dai batun rashin bayyanarsa a ƙasar nan na ci gaba da tayar da tambayoyi a fagen siyasar Nijeriya

Rahotanni da ke yawo duk da cewa ba a tabbatar da su ba sun kuma nuna cewa El-Rufai na ci gaba da hulɗar siyasa daga ƙasashen waje. Wannan lamari ya haifar da ce-ce-ku-ce, ganin cewa shi kansa ya taɓa yin kira da a riƙa bin doka da ɗaukar alhaki a shugabanci.

A wani bangare, jawabin da aka karanta a madadinsa a Taron Tattaunawa  karo ma 23 wanda Jaridar Daily Trust ta gudanar a Abuja a makon  daya gabata ya sake jawo hankali, inda aka soki rashin alhaki da tabarbarewar shugabanci da binciken majalisa ya danganta da gwamnatinsa.

A halin yanzu, Jihar Kaduna na ci gaba da sabon salo a ƙarƙashin Gwamna Uba Sani, inda rahotanni ke nuna  cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali kan sulhu, kwanciyar hankali da haɗin kai.
 

No comments