Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mahaifin Tagwayen Da Suka Rasu Bayan Rigakafi Ya Buƙaci Gwamnati Ta Bi Masa Haƙƙin Sa

Hankula sun tashi a jihar Legas bayan mutuwar tagwaye ’yan watanni tara da haihuwa ƙasa da awanni 24 bayan an yi musu rigakafin yau da kullu...



Hankula sun tashi a jihar Legas bayan mutuwar tagwaye ’yan watanni tara da haihuwa ƙasa da awanni 24 bayan an yi musu rigakafin yau da kullum a wata cibiyar lafiya ta gwamnati da ke Ƙaramar Hukumar Ojo.

Rahotanni sun nuna cewa tagwayen, da aka sanya wa suna Testimony da Timothy, sun karbi allurar rigakafi ne a cibiyar lafiya ta Ajangbadi da safiyar ranar 24 ga Disamba, 2025, sai dai suka rasu washegari da safiyar Kirsimeti, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce da kiran a binciki gaskiyar abin da ya faru.

Mahaifinsu, Samuel Alozie, wanda aka fi sani da Promise Samuel a kafafen sada zumunta, ya bayyana cewa ’ya’yansa sun kamu da matsanancin rauni da kasala jim kaɗan bayan an yi musu allurar, kuma ba su ƙara farfaɗowa ba.

A cewarsa, tagwayen suna cikin ƙoshin lafiya kuma suna motsi kafin rigakafin. Amma bayan an yi musu allurar, sai suka fara nuna gajiya da kasala ba tare da wata alama ta murmurewa ba.

“Bayan an yi musu allurar, sun zama marasa ƙarfi sosai. Wata ma'aikaciyar jinya ta ce idan zafin jikinsu ya ƙaru, na ba su paracetamol,” inji shi.

Ya ce ya bi wannan shawarar, amma maganin bai yi musu wani anfani ba. “Maganin ya ƙara raunana su matuƙa har ba sa iya cin abinci, ba sa wasa, ba sa yin halayensu na yau da kullum,” inji Alozie.

Bayan ƙasa da awanni 24, wato da safiyar 25 ga Disamba, aka ce tagwayen sun rasu, lamarin da ya girgiza iyali da al’umma baki ɗaya.

Lamarin ya sauki hankalin jama’a sosai bayan mahaifin ya wallafa bidiyo a shafukan sada zumunta, inda aka nuna gawarwakin ’ya’yansa a cikin jakunkunan gawa daban-daban. A wasu bidiyon, ya yi bayani dalla-dalla kan yadda abin ya faru tare da bayyana shakku kan tsarin rigakafin da aka yi musu.

Alozie ya zargi cibiyar lafiyar da sakaci, yana mai cewa wataƙila allurar da aka yi musu ta riga ta lalace, ta bogi, ko kuma an yi musu da yawa fiye da kima. Ya kuma ce an ba su maganin ƙwari ba tare da saninsa ko izininsa ba.

“Kafin ka kai yaro rigakafi, ka tabbata ka san irin abin da ake yi masa,” inji shi. “Ina zargin wataƙila an yi musu da yawa ko kuma magungunan ba su da inganci.”

Ya kuma nuna damuwa kan ma'aikaciyar jinyar da ta yi musu allurar, inda ya ce ba ita ce wadda ya saba gani ba. “Wadda nake saba gani tana yi mana allura ba ita ce ta yi musu wannan ranar ba. Fuska ce daban,” inji shi.

Mahaifin ya musanta iƙirarin da ake cewa jami’an cibiyar lafiya sun yi, na cewa wai gurbataccen abinci ne ya kashe ’ya’yansa. “Sun ce kwayoyin cutar abinci ne suka kashe su. Ta yaya cutar abinci za ta kashe jarirai haka?” ya tambaya.

Zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Legas ko Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta jihar kan wannan lamari. Sai dai Alozie ya ce an yi binciken gawarwaki, amma yana shakku kan gaskiya da sahihancin sakamakon.

“Ina tsoro saboda ban san ko wannan gwamnati za ta yi min adalci ba. Gwamnati ce da gwamnati,” inji shi. “Ina tsoron kada a canja sakamakon binciken.”

Mahaifin da ke cikin jimami ya roƙi lauyoyi, ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam da sauran jama’a da su taimaka masa, yana mai cewa ba shi da ƙarfin kuɗi da zai kai ƙara shi kaɗai ba.

“Idan kai lauya ne, lauya mai kare hakkin bil’adama, don Allah ka taimaka min. Ba ni da lauya. Ina neman adalci ga waɗannan yara,” inji shi, yana mai jaddada muhimmancin ɗaukar mataki domin kare amincewar jama’a ga shirin rigakafi na ƙasa.

No comments