Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Jajanta Rasuwar Malamin Nan Da Ya Ceci Wasu Kiristoci Na Jihar Filato

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini da jimamin rasuwar Imam Abdullahi Abubakar, Babban Limamin ƙauyen Nghar da ke Ƙaramar Huku...


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini da jimamin rasuwar Imam Abdullahi Abubakar, Babban Limamin ƙauyen Nghar da ke Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato, wanda ya rasu yana da shekaru 92 a duniya.

Marigayi Imam Abdullahi Abubakar ya shahara a matakin ƙasa da duniya bayan da ya ɓoye tare da kare rayukan Kiristoci sama da 200 a shekarar 2018, a lokacin rikicin ƙabilanci da na addini da ya addabi Jihar Filato.

A cikin wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa, Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen bawan Allah kuma fitaccen jagoran addini, wanda rayuwarsa ta kasance shaida ta gaskiyar imani, jarumta da girmama darajar rayuwar ɗan Adam.

Shugaban Ƙasar ya ce, “A wani lokaci da rikicin ƙabila da na addini suka mamaye tunani da hankali, Imam Abubakar ya tsaya tsayin daka a kan tafarkin zaman lafiya, tausayi da kishin dan Adam.”

Ya ƙara da cewa, duk da barazanar da ke tattare da hakan ga rayuwarsa, Limamin ya zaɓi ɗan Adam fiye da rarrabuwar kai, soyayya maimakon ƙiyayya, da rungumar juna maimakon ƙin yarda da juna. 

Shugaba Tinubu ya ce wannan jarumta tasa ta wuce wa’azi, tana aika saƙo mai ƙarfi ga duniya baki ɗaya kan ma’anar sahihin imani.

Tinubu ya jaddada cewa wannan gagarumin aiki na Imam Abubakar bai tafi a banza ba, domin ya samu lambobin yabo da karramawa a cikin gida da ƙasashen waje, sakamakon jajircewarsa wajen inganta zaman tare cikin fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Shugaban Ƙasar ya yi kira ga shugabannin addini da na al’umma da su yi koyi da rayuwar marigayin, tare da koyar da ruhin haƙuri, mutunta juna da zaman lafiya a tsakanin jama’a.

A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa Imam Abdullahi Abubakar, Ya kuma saka masa da alheri bisa kyawawan ayyukansa da jarumtar da ya nuna a rayuwarsa.
 

No comments