Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo Nijeriya a jiya Asabar bayan halartar taron Abu Dhabi Sustainability Week na shekarar 2026 (ADSW2026...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo Nijeriya a jiya Asabar bayan halartar taron Abu Dhabi Sustainability Week na shekarar 2026 (ADSW2026) tare da wasu daga cikin ministocinsa a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).
A gefen taron, Nijeriya ta sanya hannu kan Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki (CEPA) da UAE, wadda aka ce za ta ƙara zurfafa alaƙar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu.
Yarjejeniyar na da nufin bunƙasa kasuwanci da zuba jari tsakanin Nijeriya da UAE, da ƙarfafa musayar fasaha, tare da faɗaɗa haɗin gwiwa a muhimman fannoni kamar makamashi, gine-gine, noma, hakar ma’adanai da kuma makamashi.
Da yake jawabi a taron, Shugaba Tinubu ya sanar da cewa za a shirya taron INVESTOPIA na haɗin gwiwar Nijeriya da UAE a birnin Lagos a watan Fabrairun wannan shekara, domin jawo hankalin masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya.
Haka kuma, Shugaban Ƙasar ya bayyana wa mahalarta taron cewa Nijeriya na da burin tattara kusan dala biliyan 30 a duk shekara daga kuɗaɗen da suka shafi sauyin yanayi da masana’antu masu amfani da makamashi mai tsafta, yayin da take hanzarta sauye-sauyen makamashi da kuma faɗaɗa wutar lantarki a faɗin ƙasar.
Shugaba Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yin amfani da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa wajen samar da ci gaba mai ɗorewa da inganta rayuwar al’ummar Najeriya.

No comments