Gwamnatin Jihar Kaduna ta sake jaddada ƙudirin ta na tabbatar da tsaro da kuma samar da ci gaba a fannoni daban-daban na rayuwar al’ummar j...
Gwamnatin Jihar Kaduna ta sake jaddada ƙudirin ta na tabbatar da tsaro da kuma samar da ci gaba a fannoni daban-daban na rayuwar al’ummar jihar.
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ne ya bayyana hakan yayin wani taron ƙaddamar da littafi da ke ɗauke da nasarorin da gwamnatin sa ta samu cikin shekaru biyu na mulki wanda ƙungiyar 14-14 ta wallafa littafin.
Uba Sani wanda shugaba ma’aikatar fadar gwamnatin Jihar Kaduna, Malam Sani Liman Kila, ya wakilta ya ce gwamnatin Sanata Uba Sani ta himmatu matuƙa wajen inganta rayuwar al’ummar jihar ta hanyar aiwatar da manyan ayyuka a fannoni kamar ilimi, lafiya, tsaro da sauran muhimman ayyukan raya ƙasa.
Ya jaddada cewa gwamnatin Uba Sani gwamnati ce ta kowa da kowa, wadda ba ta nuna bambanci na jam’iyya, ƙabila ko addini, inda ya ce sun mayar da hankali wajen samar da abubuwan ci gaban jihar.
Malam Sani Liman Kila ya yabawa kungiyar 14-14 bisa kokarinta na wallafa littafin, inda ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen bayyana ayyuka da nasarorin da gwamnatin ta cimma ga al’umma.
Ya kuma yi kira ga ɗaukacin al’ummar Jihar Kaduna da su ci gaba da bai wa gwamnatin Sanata Uba Sani cikakken goyon baya domin cimma muradun zaman lafiya, tsaro da cigaban jihar gaba daya.

No comments