Shugaban Ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya jaddada ƙudirin ƙasarsa na saka jarin da ya kai dala biliyan 5 a fannin kasuwanci da Najer...
Shugaban Ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya jaddada ƙudirin ƙasarsa na saka jarin da ya kai dala biliyan 5 a fannin kasuwanci da Najeriya. Shugaba Erdogan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Ankara, yayin taron manema labarai na haɗin gwiwa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a yayin ziyarar aiki ta Shugaban Najeriya zuwa Turkiyya.
Shugaba Erdogan ya ce an soma tattaunawa kan cimma wannan buri, tare da amincewa da kafa Kwamitin Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki da Kasuwanci (Joint Economy and Trade Committee) tsakanin ƙasashen biyu, domin faɗaɗa damar kasuwanci da ƙarfafa zuba jarin ‘yan kasuwar Turkiyya a Najeriya.
Ya yaba da jajircewa da ƙudirin Shugaba Tinubu wajen jawo zuba jari, yana mai cewa halartar ministoci da manyan jami’ai daga Najeriya wata bayyananniyar shaida ta wannan aniya.
A cewarsa:
“Mun yi cikakken nazari kan dangantakarmu da Shugaban Najeriya da tawagarsa, musamman a fannonin kasuwanci, zuba jari, makamashi, ilimi da masana’antar tsaro. Mun tattauna matakan da za a ɗauka domin cimma burin dala biliyan 5, tare da tallafa wa zuba jari a Najeriya. Mun yi imanin cewa kafa Kwamitin Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki da Kasuwanci zai taka muhimmiyar rawa.”
Shugaba Erdogan ya yaba da sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ke jagoranta a fannin makamashi, wanda ya taimaka wajen sake fasalin tattalin arzikin Nijeriya. Ya kuma yi fatan cewa haɗin gwiwar Kamfanin Man Fetur na Turkiyya (TPAO) da abokan aikinsa a Najeriya zai haifar da sakamako mai kyau.
Dangane da barazanar ta’addanci a Najeriya da yankin Sahel, Shugaba Erdogan ya tabbatar da goyon bayan Turkiyya, yana mai cewa ƙasarsa na da kwarewa a yaki da ta’addanci.
“Ƙungiyoyin ta’addanci a yankin Sahel na barazana ga zaman lafiyar Afirka baki ɗaya. Muna tare da al’ummar Najeriya a wannan yaki, kuma a shirye muke mu ƙara haɗin gwiwa a fannonin horas da sojoji da musayar bayanan sirri,” in ji shi.
A nasa jawabin, Shugaba Tinubu ya nuna godiya ga Turkiyya kan buɗaɗɗiyar zuciya da shirinta na haɗin gwiwa domin ƙarfafa ‘yanci, zaman lafiya da walwala a duniya. Ya jaddada muhimmancin gina tattalin arziki da ya haɗa kowa da kowa, musamman masu rauni.
Ya ce: “Abu mafi muhimmanci shi ne kasuwanci ba tare da shinge ba, da ba wa masu son aiki da koyo dama. Ta yaya za mu gina tattalin arziki mai haɗa kowa? Ta yaya za mu shigar da masu rauni cikin tattalin arziki? Ta yaya za mu tabbatar da zaman lafiya a duniya?”
Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa Najeriya za ta ci gaba da taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka, duk da ƙalubalen tsaro a yankin.
A ƙarshen taron, ƙasashen biyu sun yi yarjejeniyoyi guda tara, ciki har da:
– Yarjejeniya kan manufofin ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje (Diaspora Policy)
– Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Tsaro
– Sanarwar Kafa Kwamitin Tattalin Arziki da Kasuwanci
– Yarjejeniya kan ingantaccen tsarin Halal
– Haɗin gwiwa a fannonin ilimi, kafofin watsa labarai da sadarwa
– Haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatun Harkokin Waje da na Harkokin Mata da Jin Ƙai na ƙasashen biyu.

No comments