Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Uba Sani Da Matakan Da Ya Ɗauka Na Inganta Jami'ar ABU Zariya

Daga Hashim Muhammad Suleiman, PhD Batun dangantakar Gwamnatin Jihar Kaduna da Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, na sake ɗaukar sabon salo...



Daga Hashim Muhammad Suleiman, PhD

Batun dangantakar Gwamnatin Jihar Kaduna da Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, na sake ɗaukar sabon salo a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani, inda masu ruwa da tsaki ke ganin bambanci mai ƙarfi idan aka kwatanta da abin da ya wakana a mulkin da ya gabata.

Marubucin wannan  muƙala ya bayyana cewa, duk da cewa ba ɗan siyasa ba ne, yana girmama siyasa da ’yan siyasa saboda irin ikon da suke riƙe da shi, ikon da ke shafar rayuwar al’umma baki ɗaya.

A cewar sa, yadda ake amfani da wannan iko ko ta alheri ko akasin haka shi ne ke bayyana hakikanin shugabanci.

A zamanin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, rahotanni sun nuna cewa dangantaka ta yi tsami tsakanin gwamnatin jiha da Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. A wancan lokaci, an ƙaƙaba wa ma’aikatan jami’ar nauyin haraji mai tsanani, tare da yunƙurin ƙwace wasu filayen Jami’ar da ke harabar Mando, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin Jami’ar, ASUU-ABU da gwamnatin jiha.

Masu sharhi sun nuna cewa duk da kasancewar El-Rufa’i tsohon ɗalibi ne a ABU, an samu matsaloli masu yawa a dangantakar bangarorin biyu, inda sai da tsoma bakin ƙungiyoyi da masu ruwa da tsaki aka dakatar da wasu matakai da ake ganin za su yi illa ga ci gaban jami’ar.

Sai dai a sabon salon da Gwamna Uba Sani ya ɗauka, wata hanya ce ta daban. Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta fara aiwatar da ayyukan sake ginawa da faɗaɗa hanyoyi a cikin harabar ABU, Zariya, domin inganta muhallin koyarwa da koyo. Gwamnan ya halarci jami’ar da kansa domin ƙaddamar da aikin, lamarin da ya samu yabo daga ɗalibai, ma’aikata da al’ummar gari.

Haka kuma, Gwamna Uba Sani ya kafa wani kwamitin musamman domin sake duba batun harajin da ake karba daga ma’aikatan jami’ar, harajin da ake zargin ya yi wa jami’ar nauyi a baya. Ana sa ran wannan mataki zai rage raɗaɗin da ma’aikata ke fuskanta tare da samar da fahimta tsakanin jami’ar da gwamnatin jiha.

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa wannan sabon tsari ya nuna yadda iko ke sauyawa daga lokaci zuwa lokaci, da kuma yadda shugabanni ke bambanta wajen amfani da ikon da aka damka musu. A yayin da wasu ke amfani da iko ta hanyar matsin lamba, wasu kuma na ganin iko a matsayin wata dama ta gina al’umma da tallafa wa cibiyoyin ilimi.

A ƙarshe, ra’ayin ya jaddada cewa Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, a matsayinta na uwa ga dubban ’ya’ya da jikoki, ba ta mantawa da yadda ake mu’amala da ita ko da alheri ko da akasin haka. Masu sharhi na cewa al’umma za ta ci gaba da tuna irin rawar da shugabanni ke takawa wajen daukaka ko durkusar da manyan cibiyoyin ilimi a Nijeriya.

 

No comments