Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

KIRSIMETI: Uwargidan Gwamna Zamfara Ta Raba Wa Matan Kiristoci Da Ƙungiyoyi 26 Abinci Da Kuɗaɗe

Daga Hussaini Yero Funtua, Gusau Uwargidan gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta gwangwaje matan Kiristoci da wasu ƙungiyoyi ...


Daga Hussaini Yero Funtua, Gusau

Uwargidan gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta gwangwaje matan Kiristoci da wasu ƙungiyoyi 26 da abinci da kuɗi don yin shagulgulan Kirsimeti.

Da ta ke raraba kayayyakin a Gusau ajiya  Litinin, Uwargidan gwamnan ta buƙaci 'yan uwa Kiristoci da su ci gaba da wa'azin hadɗin kai da zaman lafiya tsakanin mabiya su".

A ranakun Bukukuwan, Hurriya Dauda ta buƙaci su ci gaba da kasancewa ginshiƙan ci gaban ƙarfafa zaman lafiya a gidajen su da al'ummomi. 

Al'ummomin ƙabili da ƙungiyoyi 26 da suka ci gajiyar kyautar Bukukuwan Kirsimet waɗanda suka haɗa da Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), Ibo, Yarabawa, Dakkarawa, Igala da da Ibira".

Sauran kuma sun haɗa da Mata 'Yan  Kasuwa, Lauyoyi, Matasa, Malamai, Likitoci, Ma'aikatan Jinya, Ma'aikatan Banki, Kafafen Yaɗa Labarai da Sojoji.

Wakilun mu ya shaida mana cewa n raba Naira Miliyan 1.4, sukari, buhu 14 na Shinkafa mai nauyin kilogiram 50, Kwali na Maggie, kwali 2 na man girki da sauran su, duk an bayar da su ne don tallafa wa 'yan uwa Kiristoci a wannan lokacin bukukuwa.

Huriyya Dauda ta kuma jan kunne ga waɗanda aka ɗora ma alhakin rabon waɗannan kaya da su yi da tsoron Allah, domin manufar wannan taron, shi ne taimaka wa da ɗaga darajar gidaje waɗanda ke bikin Kirsimeti a faɗin jihar.

A jawabin ta, Wakiliyar ƙungiyar CAN, Miss Lolo Isa, ta bayyana farin cikin ta da wannan kyautar, inda ta ce hakan ya nuna cewa akwai haɗin kai a wannan gwamnatin mai albarka ƙarƙashin gwamna Dauda Lawal'.

Lolo Isa ta ce 'yan uwa Kiristoci a jihar sun yaba da ƙoƙarin Gwamna Dauda Lawal na kawo ci gaba mai ma'ana ga jihar.

CAN ta kuma bayar da kyautar yabo ta musamman kan ayyukan jin ƙai ga matar Gwamnan jihar saboda kyakkyawan aikin da ta yi wajen ci gaban mata da sauran ƙungiyoyi masu rauni a jihar.
 

No comments