Daga Zubairu Lawal,Lafia Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana shirin ta na farfaɗo da shuke-shuken sarrafa shara guda biyu da ke Lafia da Kar...
Daga Zubairu Lawal,Lafia
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana shirin ta na farfaɗo da shuke-shuken sarrafa shara guda biyu da ke Lafia da Karu.
Sakataren Hukumar Kula da Shara da Tsabtace Muhalli ta Yammacin Jihar Nasarawa, Christopher Abari ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai bayan aikin tsaftar ta ƙarshen watan Nuwamba da aka gudanar a Lafia.
Abari ya ce shuke-shuken da ke Angwan Rere a Lafia da Auta Balefi a Karu sun daɗe ba a amfani da su yadda ya kamata, amma yanzu gwamnati tana shirin dawo da su cikin aiki sosai.
Ya bayyana cewa an samu raguwar ayyuka a waɗansu wuraren, amma ana ƙoƙarin farfaɗo da su domin a fara sarrafa shara yadda ya kamata.
Sakataren ya ce farfaɗo da shuke-shuken na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka don inganta kula da shara, rage gurbatar muhalli, da tabbatar da lafiyar al’umma.
Ya ƙara da cewa za a samar wa shuke-shuken da kayan aiki na zamani domin inganta sarrafa shara yadda ya dace.
Haka kuma, ya bayyana cewa hukumar ta raba kwandunan shara na nau’o’i daban-daban a wurare da dama a cikin Ƙananan Hukumomi 13 na jihar domin saukaka zubar da shara.
Ya ce, “Ma’aikatan mu suna ci gaba da kwashe shara a kai-a kai a wuraren zubar da shara, kuma muna kira ga jama’a su rika fitar da shararsu zuwa wuraren da aka tanada domin kauce wa yaɗuwar cututtuka.”
A nasa bangaren, Abubakar Mohammed, babban mai gurfanarwa na ma’aikatar, ya ce an kama mutane 96 da suka karya dokar tsaftar muhalli a cikin Ƙananan Hukumomi 13 na jihar.
Ya bayyana cewa an kama su ne saboda gudanar da harkokin su na kasuwanci a lokacin aikin tsaftar da ake gudanarwa.
Ya ƙara da cewa hakan ya saba wa sashe na 9(2) na Dokar Tsaftar Muhalli ta Jiha.
Mohammed ya ce an gurfanar da masu laifin a gaban kotunan tafi-da-gidanka da ke Ƙananan Hukumomin su domin zama izina ga sauran jama’a.

No comments