Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DA ƊUMI-ƊUMI: Tinubu Ya Naɗa Janar Musa A Matsayin Ministan Tsaro

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Christopher Gwabin Musa, a matsayin sabon Ministan Tsaro. Mai ...




Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Christopher Gwabin Musa, a matsayin sabon Ministan Tsaro.

Mai ba Shugaban qasa shawara kan Yaɗa Labarai da Dabara, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

A cewar sa, Tinubu ya sanar da Majalisar Dattawa ta hannun Shugabanta, Godswill Akpabio, cewa Janar Musa zai gaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus daga mukaminsa ranar Litinin bisa dalilan lafiya.

Janar Christopher Gwabin Musa mai shekaru 58 ya rike mukamin Babban Hafsan Tsaro daga shekarar 2023 zuwa Oktobar 2025. Ya kuma lashe lambar yabo ta Colin Powell Award for Soldiering a shekarar 2012.

An haifi Janar Musa a Jihar Sakkwato a shekarar 1967, inda ya yi karatu a matakin firamare da sakandare, kafin ya wuce Kwalejin Karatun Gaba da Sakandare da ke Zariya. Ya kammala karatu a shekarar 1986, sannan ya shiga Nigerian Defence Academy a wannan shekarar, inda ya samu digirin Kimiyya a 1991.

An ba shi mukamin Kwamishin Soja a matsayin Laftanar na Biyu cikin Rundunar Sojojin Qasa ta Najeriya a 1991, inda ya rike muqammi daban-daban masu mahimmanci a tsawon aikinsa. Daga cikin muqammin akwai Babban Ma’aikacin Horarwa da Ayyuka na Ronduna ta 81, Kwamandan Bataliya ta 73, Mataimakin Daraktan Bukatun Ayyuka a Sashen Manufofi da Tsare-tsaren Sojojin Qasa, da kuma Wakilin Rundunar Infantri a Hedikwatar Rundunar Tankoki.

A shekarar 2019, ya riƙe muƙamin Mataimakin Babban Hafsan Horarwa da Ayyuka a Hedikwatar Cibiyar Infantri, Kwamandan Sashi na Uku na Aikin Lafiya Dole, da kuma Kwamandan Sashi na Uku na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Ƙasashe a yankin Tafkin Chadi.

Janar Musa, mai shekaru 58 da haihuwa a ranar 25 ga Disamba, ya kasance ɗaya daga cikin manyan Hafsoshin soja da suka yi fice a ayyukan soja tun bayan shiga rundunar a shekarar 1991. Ya kasance Babban Hafsan Tsaro daga 2023 zuwa watan Oktoban 2025, tare da samun kyaututtuka da dama ciki har da Colin Powell Award for Soldiering a 2012.

Tun daga lokacin, Janar Musa ya riƙe muƙamai da dama a rundunar soja, ciki har da Babban Jami’i mai lura da horo da ayyuka a Hedikwatar Runduna ta 81, Kwamandan Bataliya ta 73, da Mataimakin Darakta a Sashen Tsare-tsaren Runduna.

A 2019 ya jagoranci Sector 3 na Operation Lafiya Dole da kuma Multinational Joint Task Force a yankin Tafkin Chadi. Daga bisani, a 2021, aka nada shi Kwamandan Operation Hadin Kai, sannan ya jagoranci Rundunar Infantry kafin Shugaba Tinubu ya nada shi Babban Hafsan Tsaro a 2023.

A wasiƙar da ya aika Majalisar, Shugaba Tinubu ya bayyana ƙwarin gwiwar sa da cewa Janar Musa zai ƙara ƙarfafa wa Ma’aikatar Tsaro gwiwa tare da taimaka wa gwamnati wajen inganta tsaron ƙasa.

A shekarar 2021, an naɗa shi Kwamandan Babban Fagen Aikin Operation Hadin Kai. Daga baya ya zama Kwamandan Rundunar Infantri ta Sojojin Ƙasa kafin Tinubu ya nada shi Babban Hafsan Tsaro a shekarar 2023.

A wasiƙar da aka tura wa Majalisar Dattawa, Tinubu ya bayyana cikakkiyar qwarin gwiwarsa kan qwarewar Janar Musa wajen jagorantar Ma’aikatar Tsaro da kuma qara ƙarfafa tsarin tsaron Nujeriya.

No comments