Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

UNODC Ta Ayyana Kaduna A Matsayin Jihar Da Ta Fi Kowace A Wajen Rigakafi

Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi da Laifuka (UNODC) ta ayyana Jihar Kaduna a hukumance a matsayin misali  wajen r...

Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi da Laifuka (UNODC) ta ayyana Jihar Kaduna a hukumance a matsayin misali  wajen rigakafin shaye-shaye da kula da masu fama da jarabar ƙwayoyi, tare da yaba wa sabbin sauye-sauyen da jihar ta yi da kuma cikakkiyar dabarar ta wajen magance matsalolin amfani da miyagun ƙwayoyi da kuma ƙalubalen lafiyar ƙwaƙwalwa.

A wata wasiƙa da Wakilin UNODC a Nijeriya, Mista Cheikh Toure ya rattaba wa hannu, wacce aka tura wa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, hukumar ta yaba wa jihar bisa “muhimman ci gaba” da ta samu wajen ƙarfafa shirye-shiryen bangarorin gwamnati da na al’umma.

A cewar UNODC, wannan tsarin haɗin gwiwar da Kaduna ta ƙirƙira wanda ya haɗa maganin jarabar ƙwayoyi da lafiyar ƙwaƙwalwa a ƙarƙashin hukuma guda ya yi daidai da ƙa’idodin duniya, kuma ya kasance ɗaya daga cikin mafi inganci a matakin jihohi a Nijeriya.

UNODC ta kuma yaba da yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ke mai da hankali kan rigakafi, magani, farfaɗowa, wayar da kai da kuma haɗin kai tsakanin sassa daban-daban, tare da shiga al’umma da tallafin zamantakewa. Wannan ingantaccen tsari, in ji ta, alamar shugabanci mai hangen nesa ne da jajircewa wajen inganta yaki da jarabar ƙwayoyi.

Hukumar ta bayyana cewa jihohi da dama ciki har da Yobe, Borno, Bayelsa da  Kwara sun nemi jagorar UNODC domin kwaikwayon abin da ake kira “Samfurin Kaduna,” wanda yanzu ake ɗauka a matsayin babban tsari na dorewa da inganci wajen yaki da shaye-shaye a. Nijeriya .

Wannan ƙaruwa na sha’awa, in ji UNODC, ya ƙara tabbatar da matsayin Kaduna a matsayin jagora da mai kirkira wajen gyaran harkokin kiwon lafiya da farfadowar al’umma.

A ƙarshe, UNODC ta sake tabbatar da cewa za ta ci gaba da tallafawa Jihar Kaduna ta hanyar horo, gina ƙwarewa, da haɗa shirye-shirye da manufofin ƙasa da na yankin yaki da shaye-shaye. Ta kuma yi alkawarin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarta da Gwamnatin Jihar da KadSAMHSA domin inganta tsare-tsare masu tushe na bincike wajen rigakafi da magance jaraba.
 

No comments