Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Amince Da Murabus Ɗin Ministan Tsaro

Ministan Tsaron Nijeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya ajiye muƙamin sa nan take, bisa dalilai na lafiya. A cikin wata wasiƙa da aka ...


Ministan Tsaron Nijeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya ajiye muƙamin sa nan take, bisa dalilai na lafiya.

A cikin wata wasiƙa da aka rubuta ranar 1 ga Disamba zuwa ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Badaru ya bayyana cewa ya yanke shawarar janyewa daga kujerar minista ne domin mayar da hankali kan lafiyar sa.

Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin nasa, tare da gode masa bisa gudunmawar da ya bayar wa ƙasar tun bayan nadin da aka yi masa a ranar 21 ga Agusta 2023.

Daga cikin bayanan da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Shugaba Tinubu zai tura sunan wanda zai maye gurbin Badaru zuwa majalisar dattawa a cikin wannan makon.

Badaru Abubakar, wanda ya kai shekara 63, ya shugabanci jihar Jigawa na tsawon wa’adi biyu daga 2015 zuwa 2023, kafin nadinsa a matsayin Ministan Tsaro.
 

No comments